DiscoverMadubin Usman Kabara
Madubin Usman Kabara
Claim Ownership

Madubin Usman Kabara

Author: Usman Kabara

Subscribed: 8Played: 11
Share

Description

Ina hira da kowa a kan komai don fahimtar rayuwa.
77 Episodes
Reverse
Karatu ne ya kawo iyayenta 'yan asalin jihohin Kano da Jigawa zuwa Amurka daga a Najeriya, amma kuma kaddarar zama ta kama su har suka hayayyafa. Iman ta fada min yadda take da burin zaman Najeriya duk kuwa da cewa a Amurka aka haifeta ta girma.
Ali Nuhu | MUK Na 2

Ali Nuhu | MUK Na 2

2025-11-1112:09

Na yi hira da Ali Nuhu Mohammed jarumin fina-finan Hausa da Turanci na Najeriya a lokacin da ya ziyarci birnin Washington DC da ke Amurka,, in da na tambaye shi darussan da ya koya a cikin shekaru 20 da ya kwashe yana harkar shirya finafinai.
Munira Sulaiman Tanimu

Munira Sulaiman Tanimu

2020-12-0745:00

@meemaestee1 Tana daya daga cikin zaratan matasan mata a Arewacin Najeriya da ta ciri tuta a bangaren ilimi, sana’o’i, siyasa, tallafawa ilimin ‘ya’ya mata ‘yan talla. Mun tattauna da ita don jin tarihin rayuwarta da kalubalen da ta fuskanta. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support
Abubakar Malami

Abubakar Malami

2020-12-0730:22

Ministan shari’a na Najeriya ya ba wa Madubin Kabara tarihin rayuwarsa tun daga kuruciya har zuwa girmansa da yadda aka yi ya zama masanin shari’a har zuwa zama alkali da ma yadda aka yi ya koma cin gashin kansa a matsayinsa na lauya. Har da yadda aka yi ya taka matsayin daraja magi girma a aikin lauya a Najeriya lokacin da yake da karancin shekaru ba kamar yadda aka saba gani tsofaffin lauyoyi na samu ba. Bugu da kari mahaifinsa ma ya babban alkali ne. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support
Halima Idris (Bachure)

Halima Idris (Bachure)

2020-09-0115:02

Mun tattauna da matashiyar da ke ba wa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i shawara game da zane-zane da kere-kere ko kirkira. Mun yi wannan tattaunawar ne da ita ne a watannin baya da ta kawo ziyara a birnin Washington DC na Amurka. A biyo mu a ji ko ta yaya matasa ke samun wakilcin Halima da ake wa lakabi da Queen. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message
Jamila Kabiru Fagge

Jamila Kabiru Fagge

2020-08-0340:40

Jamila Kabiru Fagge ba’amurkiya ce ‘yar asalin Najeriya, wacce ta girma tsakanin kasashen biyu, sannan ta gano wasu bambance-bambance a yanayin yadda muke tarbiyyantar da ‘ya’yanmu musamman game da ilimantar da su sanin jinsi da kuma darajar gabobi da sassa jikin maza da mata. Ta bayyana wa Madubin Kabara yadda iyayenta suka reneta da yadda kuma take rainon nata ‘ya’yan. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message
Ali Nuhu

Ali Nuhu

2020-07-2317:16

Idan aka yi maganar fina-finan Najeriya musamman na farfajiyar Arewaci da a ke wa lakabi da Kannywood, to har abada tarihi sai ya sako Ali Nuhu cikin fitattun taurarin da suka zama daga cikin zubin farko-farkon harkar. A cikin shekarar nan ne ya cika shekaru 20 da fara fitowa a fina-finan nasu. Wannan ne dalilin da yasa muka masa tambayar darasin da ya koya a tsawon wannan lokaci. Mun hadu da jarumin ne a wata ziyarar da ya kawo birnin Washington DC. A yi sauraro lafiya. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message
Daga yanzu Madubin Usman Kabara podcast zai dinga zuwa muku ne a tsarin shiri mai fitowa zango-zango, inda zamu saki zangon na 1 a mako mai zuwa ranar Juma’a 9 ga watan Janairun shekarar nan ta 2026. Kadan daga cikin bakin wannan zangon sun hada da:1. Prof. Abdalla Uba Adamu2. Umar M. Shareef3. Hon. Zainab Buba 4. Hon. Saudatu Sani5. Maryam Booth6. Zaaki AzzayKu yi following dina ta nan a kyauta don jin yadda mutane ke shan gwagwarmaya a rayuwa don mu koyi darasi ta hanyar ganin zurfin ruwa da na gaba.
Na sami zama tare da Lauya Dan Gwagwarmaya Barrister Solomon Dalung, tsohon Ministan Matasa Da Wasanni a lokacin mulkin Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari. Inda na tattauna da shi don kallon rayuwarsa a cikin shirin Madubin Usman Kabara Podcast domin daukar darasi ga ‘yan baya.
Na ziyarci Usman Umar (SojaBoy), domin yin hira da shi ido da ido a kokarina na jin dalilan salon wakokinsa da mafiya yawan mutane musamman 'yan Arewacin Najeriya, ba su yarda da salon nasa ba, suna ma kallon abin a matsayin rashin tarbiyya da rushe al'ada da addini.
Nazir Ahmed Hausawa (Ziriums), yana daya daga cikin ‘yan masana’antar finafinan Kannywood, Makadin Fiyano, Mawakin gambarar Hausa HipHop, Tsohon malamin koyar da kida, Tsohon ma’aikacin BBC World Service Trust da VOA Hausa, Masanin harkokin gidajen alfama na Amurka. A cikin hirarsa da Madubin Usman Kabara a Amurka, ya bayyana min darussan da ya koya a zamansa na shekaru a Amurka.
Na sami yin hira da shahararriyar Jarumar Fina-finan Hausa Nafisat Abdullahi a birnin Washington DC da ke Amurka, don sanin asalinta da kuma yadda take tafiyar da rayuwarta.
Na yi hira da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya, Mai Girma Sanata Barau I. Jibrin (Maliya) game da rayuwarsa da kuma gudunmawarsa a siyasance, musamman ga 'yan Arewacin Najeriya.
Kamaluddeen Kabir, dan asalin jigar Katsina ne mai digirin digirgir wanda yayi karatunsa a tsakanin Najeriya da Birtaniya sannan kuma Malami ne yanzu haka a jami'ar Umaru Musa 'YarAdua da ke jihar ta Katsina.
Mun sami tattaunawa Aminu Waziri Tambuwal gwamnan jihar Sokoto, kuma shugaban tawagar yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya a 2023 da ke tafe. Inda ya bamu labarin kuruciyarsa har zuwa girma da shiga fagen siyasa. Ba mu bar shi ba sai da ya fada mana dalilinsa na janye wa daga takarar shugabancin Najeriya don mara wa Atikun a karkashin jam'iyyar PDP.
Na'ima Idris Usman, cikakkiyar Likita ce da ke jihar Kanon Najeriya, ta yi karatun a tsakanin Najeriys da China. Ta bamu labarin rayuwarta daga kuruciya zuwa girmanta, da ma yadda aka yi ta fara ilimantar da mata ta kafafen sada zumunta game da lafiyar jikinsu duk da cewa furta kalmomin da ke da alaka da al'aura abu ne mai cike da kalubalen a kasar Hausa. Da kuma yadda karshe ta buge da zuwa shirin horar da shugabanci ga matasan Afirka a Amurka da a turance ake kira da Mandela Washington Fellowship da aka fi sani da Young African Leaders Initiative (YALI) na shekarar 2022.
Usman Umar da aka fi sani da Soja Boy mawaki ne, dan wasan kwaikwayon zahirin rayuwa da ya fito a tauraron wani shirin wasan talbijin a Amurka mai suna 90DayFiance wanda ake bibiyar saurayi da budurwa don ganin yadda alakarsu ta soyayya ke tafiya.
Aisha Hassan matashiya ce 'yar asalin jihar Neja a Najeriya da ta girma a Ingila, sannan ta yi karatu mai zurfi a fannin hada-hadar kasuwanci. Bugu da kari ba a barta a baya ba wajen shiga fagen kafafen sadarwar zamani inda take koyar da salon sa sutura da daurin dan-kwali a shafukanta na yanar gizo.
An karrama Halima Ali Shuwa da lambar yabon gama digirin digirgir a matsayin dalibar da ta yi wa sa’o’inta fintinkau a fanni binciken sojojin garkuwar jikin bil’adama. Bugu da kari kuma sai ga wani babban kamfanin hada magunguna a duniya ya bata aiki sakamakon fahimtar amfanin abin da ta kware a fannin binciken kwayar halitta.
Adamu Garba II matashi ne mai kwarin gwiwa sannan wanda ya ke dan kasuwar da yayi iliminsa a tsakanin Najeriya har zuwa Amurka. Yana daga cikin 'yan takarar Shugaban Kasar Najeriya a shekarar 2023 mafi karancin shekaru a tsakanin masu neman wannan kujera a kasar da ta fi kowa ce kasar Afirka yawan al'umma da kuma karfin arzikin man fetur. Shine kuma wanda 'yan uwa da abokan arziki suka tara wa sama da naira miliyan 80 don yin takara a jam'iyyar APC amma kwatsam sai ya canja sheka zuwa YPP.
loading
Comments