Discover
Najeriya a Yau
910 Episodes
Reverse
Send us a text A siyasar Najeriya, akwai ka’idoji da dokoki da ke tsara yadda ake gudanar da zaɓe, ciki har da lokacin da doka ta amince a fara yaƙin neman zaɓe. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, wato INEC, ita ce ke da alhakin bayyana jadawalin zaɓe da kuma ranar da ‘yan takara za su fara neman goyon bayan al’umma a hukumance. Sai dai duk da waɗannan tanade-tanade, ana ci gaba da ganin alamu da ayyuka da ke nuna cewa wasu ‘yan takara suna fara yaƙin neman zaɓe tun kafin a buga gangar siyasa. Wann...
Send us a text A cikin ‘yan kwanakin nan, siyasar Najeriya ta sake daukar sabon salo, bayan barkewar takaddama tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, da manyan shugabannin jam’iyyar (APC). Jam’iyyar APC na kallon yadda Wike — wanda ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne amma ke rike da mukami a karkashin gwamnatinta — ke yin katsalandan a harkokin jam’iyyar, musamman a matakin jihohi, a matsayin barazana ga tsarin jam’iyya da ikonta na cikin gida. Wannan lamari ya haifar da mu...
Send us a text Harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai kasuwar Daji da ke karamar hukumar Borgu a Jihar Neja ya sake jawo hankalin al’umma kan matsalar rashin tsaro da ke kara ta’azzara a yankunan karkara na Arewa ta Tsakiya. Kasuwar Daji, wadda ke zama cibiyar hada-hadar kasuwanci ga manoma, ‘yan kasuwa da mazauna kauyuka makwabta, ta kasance wuri na zaman lafiya kafin wannan mummunan lamari da ya girgiza mazauna yankin. Batutuwa da dama daga kafafen yada labarai da dama sun bayyana mabanbanta...
Send us a text A fagen siyasar Najeriya a halin yanzu, ana ta ce-ce-ku-ce kan wacce ce babbar jam’iyyar adawa da za ta iya tsayawa ƙafada da ƙafada da jam’iyyar APC mai mulki. Wannan takaddama ta fi karkata ne tsakanin jam’iyyar PDP, wacce ta dade tana taka rawa a matsayin babbar jam’iyyar adawa bayan ficewarta daga mulki a 2015, da kuma jam’iyyar ADC, wacce a ‘yan shekarun nan ta fara samun karɓuwa sakamakon shigar wasu manyan ‘yan siyasa da kuma ƙoƙarin gina sabuwar haɗaka a matsayin madadi...
Send us a text Shekarar 2026 ta zo a wani lokaci da ’yan Najeriya da dama ke fuskantar matsin tattalin arziki, da sauye-sauyen siyasa, da kuma ƙalubalen rayuwa da ke bukatar sabon tunani. Wannan ba lokaci ba ne na fatan samun sa’a kawai, lokaci ne na tsara hanya, da ɗaukar matakai, da yin gyara a rayuwar yau da kullum. A wannan shiri, za mu duba yadda ya kamata ’yan Najeriya su fara sabuwar shekara ta 2026 ta hanyoyi masu ma’ana—daga kula da yadda zasu sarrafa kuɗi da sana’a, zuwa kiwon lafiy...
Send us a text Yayin da muke bankwana da shekarar 2025, siyasar Najeriya ta kasance cike da sauye-sauye, rikice-rikice, da kuma manyan al’amura da suka shafi iko, jam’iyyu da shugabanci. Shekarar ta shaida sauyin sheƙa na ‘yan siyasa, rikicin cikin gida a wasu jam’iyyu, da kuma fafutukar karɓar ragamar mulki a jihohi da matakin tarayya, lamarin da ya ƙara zafafa siyasar ƙasa. A bangaren tsare-tsaren gwamnati kuwa, 2025 ta kasance shekara mai ɗauke da tsauraran manufofi da suka shafi tattalin ...
Send us a text A shekarar 2025, Najeriya ta fuskanci manyan ƙalubalen tsaro da suka fi daukar hankali, musamman hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da ta’addanci a jihohin Arewa kamar Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna da kuma Borno. Hare-haren sun yi sanadin rasa rayuka, da rufe makarantu, da kaura daga gidaje, da kuma durkushewar harkokin tattalin arziki a wasu yankuna. Wadannan matsaloli suka sa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro, domi...
Send us a text A duk faɗin Arewacin Najeriya, ana gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, duk da kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a yawancin yankuna. Kiristoci kan yi bukukuwansu cikin mutunta al’adar Musulmai, yayin da Musulmai kuma ke nuna goyon baya ta hanyar gaisuwa, da tsaro, da mu’amala ta zamantakewa. A wurare da dama kamar Kaduna, Jos, Zaria, Minna da wasu sassan jihar Kano, ana ganin Kiristoci suna zuwa coci ba tare da tsangwama ba, yara s...
Send us a text A yayin da al’ummar Kirista a sassa daban-daban na ƙasar nan ke gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin walwala, da annashuwa da haɗuwa da iyalai, akwai kuma waɗanda wannan lokaci ya zo musu cikin ƙunci da jimami. Waɗannan su ne mutanen da matsalolin tsaro—kamar hare-hare da rikice-rikice—suka tilasta musu barin gidajensu da muhallansu. A maimakon shagulgula a cikin gidajensu, suna gudanar da bikin ne a sansanonin gudun hijira, inda rayuwa ta cika da ƙalubale, da rashin is...
Send us a text Gabannin bukukuwan Kirsimeti, kasuwanni a sassan ƙasar nan sun cika sun bunkasa. Jama’a na ci gaba da zirga-zirga domin sayen kayan bukukuwa, yayin da ‘yan kasuwa ke kokarin jawo hankalin masu saye ta hanyar daidaita farashi. A wannan shekarar, alamu sun nuna ba a samu hauhawar farashin kayayyaki a yawancin kasuwanni ba, sai dai wasu na kokawa da rashin kudaden saye. Ko yaya hakikanin farashin kayayyakin suke a wasu kasuwannin Nnajeriya? Wannan shine batun da sh...
Send us a text Takaddama mai zafi ta dabaibaye sabbin dokokin haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su, bayan zarge-zargen cewa an samu sauye-sauye a cikin dokokin bayan an kammala dukkan matakan amincewa da su a majalisa. Batun da ya taso ya jawo cece-kuce daga ‘yan majalisa, jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula, inda suke tambayar sahihancin abin da aka mika wa Fadar Shugaban Kasa domin aiwatarwa. Masu suka na cewa sauye-sauyen da ake zargin an yi ba tare da amincewar majalisa ba...
Send us a text Gobara a irin wannan yanayi na iska musamman a kasuwanni da gidaje ba sabon abu bane kuma ba abun mamaki ba. Wasu kafintoci dake aiki a kasuwar lale dake unguwar Tal’udu a karamar hukumar Gwale dake jihar Kano sun wayi gari da alhinin gobarar da ta yi sanadiyyar raba su da hanyar abincinsu. Wannan gobara da ba’a san musabbabinta ba ta janyo asarar miliyoyin Naira tare da jefa wadanda abun ya shafa cikin mawuyacin hali. Ko wanne irin hasara aka yi a wannan gobara? Wannan...
Send us a text Murabus din da Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta kasa Ahmed Farukh ya yi daga mukaminsa ya sa ‘yan Najeriya da dama na ta tofa albarkacin bakinsu musamman a bangaren harkokin mai. Murabus din na zuwa ne bayan doguwar takaddama tsakaninsa da Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote kan batutuwa da dama. Shin ko wanne darasi za a koya daga wannan takaddama da ta kai ga murabus din shugaban. Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai y...
Send us a text Takunkumin da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya wa wasu ‘yan Najeriya ya sake jawo hankali kan irin tasirin manufofin ƙasashen waje ga rayuwar mutane da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya. Wannan takunkumi, wanda ya haɗa da hana shiga Amurka, da toshe kadarori ko hana mu’amala da wasu hukumomi da kamfanonin Amurka, ba wai hukunci ne ga mutum ɗaya kaɗai ba, kazalika yana da tasiri mai zurfi ga harkokin kasuwanci, zuba jari da martabar ƙasa a idon duniya. Ko ta y...
Send us a text Batun matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na mayar da shalkwatar Bankin Masana’antu zuwa jihar Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya. Wannan mataki ya tayar da mabanbantan ra’ayoyi daga bangarori daban-daban na al’umma, inda wasu ke kallonsa a matsayin shawara mai ma’ana da za ta karfafa harkokin masana’antu da jawo jarin cikin gida da na kasashen waje. Sai dai a daya bangaren kuma, akwai masu sukar wannan mataki, inda suma suka bayyana irin tasu damuwa ka...
Send us a text A ’yan shekarun nan, lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara—wanda a da ake ɗauka a matsayin lokacin farin ciki, da haɗuwa da iyalai, da tafiye-tafiye—ya fara sauya salo ga mutane da dama. Maimakon shirye-shiryen ziyartar ’yan uwa ko halartar bukukuwa a garuruwa daban-daban, mutane da yawa yanzu suna cike da fargaba da damuwa. Babban dalilin hakan shi ne ƙalubalen tsaro da ke ƙara tsananta a sassa daban-daban. Rahotanni na hare-haren ’yan bindiga, da sace-sace a kan manyan hanyoy...
Send us a text A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa. Tsarin ya mayar da hankali kan daidaita ranakun makaranta, da tsara lokutan darussa bisa bukatun shekaru da matakin karatu, da kuma kara aiki a ...
Send us a text A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna cin wasu tsirrai, ganye, ko ababen da ke dauke da sinadarai masu haɗari, waɗanda daga baya suke taruwa a jikinsu har su zama guba ga mutum idan aka ci su. Wasu lokuta ma waɗannan gubobi ba daga abincin dabbar suke fitowa ba, sai dai daga s...
Send us a text Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan. Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadannan ‘yansanda, akwai batun samar da kayan aiki da horo da sauran abubuwa da ake bukata don gudan...
Send us a text Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell? ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa. Ko yaya wannan dabara take aiki? Wannan s...



