DiscoverDaga Laraba
Daga Laraba
Claim Ownership

Daga Laraba

Author: Unknown

Subscribed: 3Played: 33
Share

Description

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

250 Episodes
Reverse
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su. Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa ’ya’yansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su. Mene ne dalilin hakan, yaushe kuma daga ina ya samo asali, kuma mene ne tasirinsa a al’adance da ma a addinance? ...
A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi. Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu? Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau na wannan ...
Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro. 'Yan bindigar sun yi ikirarin suna samun kimanin naira miliyan 300 duk mako daga haramtattun wuraren hakar ma’adinai. Shirin Daga Laraba ...
Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah. Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani dasu yayin bikin sallah sun yi tashin gwauron zabo inda alumma da dama ke ta bayyana damuw...
A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu. Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsalolin lafiya. Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙarin abubuwan da idan aka tara su a jiki na dogon lokaci, na iya haifar da illa. &n...
Takaddama ta dabaibaye batun wata matashiya mai suna Walida Abdullahi, bayan iyalanta sun zargi wani jami’in Department of State Services mai suna Ifeanyi Onyewuenyi da sace ta daga gidansu tare da tsare ta na tsawon lokaci ba tare da sanin inda take ba. Rahotanni sun ce ana zargin jami’in ya sauya mata addini daga Musulunci zuwa Kiristanci tare da canza mata suna zuwa Chinaza, lamarin da iyalanta suka ce an yi ba tare da yardarta ba ko kuma amincewar danginta. Haka kuma, bayan shafe lokaci...
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa. Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana.
A watan Agustan shekarar 2019, gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakokinta da wasu ƙasashe makwabta ciki har da Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin. Wannan mataki a wancan lokaci an ɗauke shi ne domin yaƙi da fasa-kwauri, hana shigo da kaya ba bisa ƙa’ida ba, da kuma kare tattalin arziƙin cikin gida. Bayan wannan tsawon lokaci da aka dauka na takaita zirga-zirga tsakanin wadannan kasashe, lamarin ya shafi kasuwanci, da mu’amalar jama’a da kuma rayuwar al’ummomin da ke zaune a kan iyaka. ...
An dade ana muhawara a tsakanin masu sana’a da masu digiri, musamman wadanda suka yi gam-da-katar suka samu ayyuka masu tasiri, kan abin da ya fi kawu samu. Ko wanne bangare yana da kwararan hujjoji; amma masu raba gardama sun ce akwai zabi na uku. Shin wanne zabi ne wannan? Abin da shirin Daga Laraba zai yi nazari a kai ke nan.
A farkon Jamhuriya ta Hudu a shekarar 1999, dawowar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya ya haifar da babban fata a zukatan ‘yan ƙasa, inda mutane suka yi tsammanin ƙarshen mulkin soja zai kawo adalci, ci gaban tattalin arziƙi, tsaro, da shugabanci nagari da ke sauraron muradin jama’a. Jama’a sun yi imanin cewa za su sami ‘yancin faɗar albarkacin baki, ingantaccen zaɓe, aikin yi, da rage talauci ta hanyar shugabannin da suka fito daga zaɓin jama’a. A cigaba da kawo muku shirye-shirye gab...
A shekarar 1999, lokacin da Najeriya ta sake komawa mulkin farar hula, tattalin arzikin ƙasa da kayayyakin more rayuwa na cikin wani yanayi na dogon mulkin soja. A wancan lokaci, masana da manazarta harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa dogaro da man fetur ya yi wa ƙasar katutu, masana’antu da dama sun tsaya cik, kuɗin ƙasa ya raunana, yayin da rashin aikin yi da talauci suka yi ƙamari. Haka kuma, a cewar manazarta, kayayyakin more rayuwa kamar hanyoyi, da wutar lantarki, da asibito...
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa. Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi. Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta mai abin hannu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan matan wannan zamanin na kin auren talaka...
Rage farashin man fetur a Najeriya na daya daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin al’umma, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ta yi wa ’yan kasa katutu a ‘yan watannin nan. Man fetur ba wai kawai makamashi ba ne da ake amfani da shi wajen tafiyar da ababen hawa; ginshiki ne da kusan dukkan harkokin tattalin arziki ke jingina da shi – daga sufuri, da samar da kayayyaki, har zuwa rabon su zuwa kasuwanni. Saboda haka, duk wani sauyi a farashin mai kan yi tasiri kai tsaye ko a kaikaice ga f...
A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan kare dangi ga Najeriya. Ko wannan ziyarar da tawagar Amurka ta kawo zai kawo karshen matsalar tsaron da Najeriya ke ciki? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba a kai.
Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa majalisar. Wannan naɗin ya zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman hare-haren ’yan bindiga, da ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci a yankuna daban-daban. Ko wadanne irin kalubale ne ke gaban sabon ministan tsaron ...
A cikin 'yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da 'yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi. Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu? Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau na wannan lo...
Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai. Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin ya kamata a yi dukkan mai yiwuwa don ganin an ceto wadannan yara ba tare da sun samu rauni ba. Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.
A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar. A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu. Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu...
Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro. 'Yan bindigar sun yi ikirarin suna samun kimanin naira miliyan 300 duk mako daga haramtattun wuraren hakar ma’adinai. Shirin Daga Laraba na wa...
Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa sun nuna adawa da niyyar Lamido na neman kujerar shugabancin PDP, suna ganin cewa ba shi ne ya dace da wannan matsayi a yanzu ba. Sai dai magoya bayan tsohon gwamnan sun bayyana wannan mataki a matsayin n...
loading
Comments