DiscoverKida, Al'adu da Fina-Finai
Kida, Al'adu da Fina-Finai
Claim Ownership

Kida, Al'adu da Fina-Finai

Author: RFI Hausa

Subscribed: 15Played: 731
Share

Description

Shirin Al’adu, kida da fina-finai,  shiri ne da ke zo maku  a ranakun assabar  da kafe 5:30 na yamma, tare da maimaici da karfe 8:00 na safiyar ranar  Lahadi.Inda muke kawo ma ku rahotanni  da labaran da  suka shafi Fina-finai na gida da ketare, firarraki  da  mawakammu na gargajiya da na zamani, tare da kawo maku  labaran da suka shafi al’adummu na gida da ketare. Tare da naku Mahaman Salisu Hamisu.

27 Episodes
Reverse
Shirin na wannan mako zai yi duba ne kan yadda Hausawa ke tafiyar da masarutar su a yankin Edo wato jihar Benin a tarayyar Najeriya Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa
Shirin wannan mako ya zagaya masana'antun fina finai dabam dabam, inda a Kannywood, wato masana'antar fina finan Hausa ta Najeriya ya kawo labarin yadda kalaman da jaruma Nafisa Abdullahi ta y a kan 'yayan da ake haifa ba a san yadda za a yi da su ba' ya janyo cece kuce, bayan da Naziru Sarkin Waka  ya yi mata raddi.
Shirin Finafinai kadekade da Al'adu, ya dauko muku kadan daga cikin abubuwan da suka faru a KANNYWOOD.Mun kuma Tattauna da mawaki MUKTAR BANDANA game da wakar (Ramadana yana ban kwana). Sai kuma bangaren Al'adu tare daTauraruwar waka OUMOU SANGARE wacce zata saki sabon album mai suna Timbuktu  ranar 29 ga wata na Afrilu bayan ta dau lokaci bata saki wata wakarba tun bayan shekarar 2017."
A shirin namu na yau zai yada zango ne a jihar Agadez dake arewacin jamhuriyar Nijar domin duba shagulgulan biyanu wata al’adar da mutan Agadez ke rayawa shekaru aru aru da suka gabata da ake kira Biyanu.Muhammed Billal mai mukamin Agolla daya daga cikin masu shirya Biyanun ya samu zantawa da rediyon Faransa rfi.
Shirin Kida da al'adun gargajiya tare da Mahaman Salissou Hamissou a wannan makon ya dora akan inda shirin ya tsaya a makon jiya, game da yadda Mamman Shata Katsina ya cika shekaru 20 da barin duniya dama tasirin wakokinsa ga bunkasuwar harshen hausa.
A Najeriya Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci karkashin jagorancin mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ita ce ta tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a jihohi da dama na kasar a yammacin jiya.Ko baya ga Najeriya, a yau ana gudanar da bukukuwan sallar a mafi yawan kasashen muslumi da suka hada da Chadi, Kamaru, Ghana, Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larawaba da dai sauransu.
Al’ummar musulmi a sassa da dama na duniya na gudanar da bukukuwan karamar sallah wato Idil Fitr a yau juma’a, bayan kammala azumin watan Ramadana.A Najeriya Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci karkashin jagorancin mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ita ce ta tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a jihohi da dama na kasar a yammacin jiya.A cikin shirin na musaman Abdoulaye Issa ya duba wasu daga cikin muhiman batutuwa da jama'a suka mayar da hankali a kai a Nijar.
Aure a duniyar hausa

Aure a duniyar hausa

2017-11-1410:27

A cikin shirin al'adu na gado Salissou Hamissou ya duba yanayin aure  a duniyar hausa.Za ku ji irin sauyi da aka samu,dama yadda mutane ke kallon halin da ake ciki.
Mawakin Gargajiya da ake kira Rogazo dai ya shahara wajen yin fira cikin wake, ya kuma gwada irin basirar da Allah ya yi masa a zantawa da Mahaman Salissou Hamisou
Haoua Kabir cikin shirin al'adun mun na gado ta duba mana yadda yan kabilar Nufawa ke rayyuwa dama zamantakewa .
Kida da Al'adun Nufawa

Kida da Al'adun Nufawa

2016-01-0920:01

Shirin Kida da Al'adu ya tattauna da Mawakiyar Nufawa Amina Ibrahim da ake kira Kashekala sannan shirin ya diba wasu al'adun Nufawa.
Shirin Kida da Al'adu ya tattauna da Lawal Musa Dankwari Malamin Hausa a Zaria wanda ya rera wake kan sauyin yanayi da ake samu a yanzu da tsabtace muhalli. Dankwari ya wake Ruwa da Daji da tsirrai da tsunsaye.
Shirin Kade-kade da Al'adu na wannan karo tare da Hauwa Kabir, ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke aure kafin zuwan musulunci. 
Shirin ''Kida da Al'adu'' tare da Hauwa Kabir, a wannan mako ya duba rayuwar shahrarrun mawakan kasar Mali Amadou da Mariama, mata da miji kuma makafi da suka yi fice sosai a fagen waka.
Kade-kade da Al'adu tare da Hauwa Kabir, shiri ne da ke ba ku labarun shahrarrun makada da mawaka tare da yin dubi a game da al'adun wasu al'ummomi.
Shirin Kade-kade da Al'adu a wannan karo, Hauwa Kabrir ta yi dubi ne a game da ''Hawa'' da sarakuna ke yi a kasar Hausa, a lokacin gudanar da bukukuwa.
A sha saurare lafiya tareda Hauwa Kabir
loading