A wannan shiri, muna karanto littafan Hausa masu ma’ana, musamman na da can, irin wadanda aka dade da wallafa su domin su tuna mana rayuwa, da al’adunmu na Hausawa kafin zuwan Turawa da ma bayan zuwansu. A cikin littafan akwai hikimomi, da dabaru, da almara, da kuma abubuwan ban mamaki, da na ban sha’awa da birgewa, da jaruman marubutan suka yi.