Discover
Al'adun Gargajiya
Al'adun Gargajiya
Author: RFI Hausa
Subscribed: 3Played: 16Subscribe
Share
© France Médias Monde
Description
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
163 Episodes
Reverse
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa. Shekaru aru-aru, da zarar an yi auren budurwa a ƙasar Hausa akan haɗata da ƙaramar yarinya da za ta yi mata zaman ɗaki, wanda a wasu lokutan anje kenan domin galibi aure ke raba wannan ƙaramar yarinya da gidan, kodayake wasu kan shafe wani wa'adi ne gabanin komawa gaban iyayensu na ainahi. Sai dai a ƴan shekarun nan wannan al'ada da kan yi tasiri wajen ƙarfafa zumunci ta zama tarihi, walau ko saboda yanayi na rayuwa, ko kuma saboda yadda aka tsagaita da auren ƴammata masu ƙarancin shekaru da dai sauran dalilai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Shirin a wannan mako ya yi tattaki ne, zuwa ƙauyen Ingal da ke Yankin Agadez a jamhuriyyar Nijar, domin waiwayar gagarumin bikin makiyaya da ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee' wanda aka saba yi duk shekara. Bikin makiyayan na Cure Salee ya gudana ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan da muke ciki na Oktoba. Manufar bikin ita ce yadda za a ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya domin kafa ginshiƙin zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu. Bikin na bana ya samu halattar ƙabilun Fulani da na Abzinawa da Larabawa a Nijar ɗin da wasu daga Najeriya, da Mali da burkina Faso da kuma Aljeriya. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman...............
Shirin al'adunmu na gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gushewar sana'ar kaɗi a ƙasar Hausa duk da kasancewarta guda cikin sana'o'in Hausawan suka gada kaka da kakanni. Galibi sana'o'in Hausawa na tafiya ne da tsarin rayuwa da zamantakewar jama'a, cikin wannan kuwa har da sana'ar kaɗi wadda galibi dattawa Mata suka fi ƙwarewa akai, kodayake wannan sana'a na gab da gushewa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan mako, ya mayar da hankali kan manufar Maita da kambun baka a mahangar al'adu da kuma addini, a wani yanayi da ake yiwa wannan abubuwa biyu mabanbantan kallo. Duk da cewa wasu na yiwa waɗannan abubuwa biyu kallon abu guda, amma a wasu na kallon abubuwan biyu a matsayin mabanbanta kasancewar guda akan sameshi ne haka suddan yayinda ɗayan kuma ake iya haifar mutum da shi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Al’adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la’akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen. Tun cikin makon jiya masana da sauran jama’ar gari ke tofa albarkacin bakunansu akan karramawar da wata Jami’a mai suna European-American University ta yi wa fitaccen mawaƙin siyasa a Najeriya Dauda Kahutu Rarara, wanda ta bai wa Digirin Girmamawa na Dakta. Reshen Jami’ar da bayanai a yanar gizo suka nuna cewar hedikwatarta na ƙasar Faransa ne ta yi bikin Karrama mawaƙi Raran ne a Abuja, ranar Asabar, 20 ga watan nan na Satumba, taron da ya samu halartar wasu fitattun mutane. Sai dai Kash! ‘yan sa’o’i bayan bikin da aka yi Jami’ar da ake alaƙanta da Turai da Amurka ta ce ba ta fa san zance ba, domin ba da yawunta aka miƙa wa fitaccen mawaƙin siyasar Digirin na Girmamawa ba, zalika dukkanin mutanen da suka yi iƙirarin alaƙanta kansu da ita ta barranta da su, domin sun yaudari mutane ne da sunanta domin samun damar karɓar na goro a huce. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda sannu a hankali sana'ar kira ke shudwa musamman ta ƴan Kabilar Abzinawa da ke jihar Agadez a jamhuriyar Nijar. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Issa.
Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya ɗora ne akan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran ƙasashen da ke da al’ummar Hausawa, bikin da sannu a hankali ya riƙa samun karɓuwa gami da faɗaɗa har zuwa wannan lokaci da ya shafe shekaru 10 cif.
Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya tattauna ne a kan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran ƙasashen da ke da al’ummar Hausawa, bikin da sannu a hankali ya riƙa samun karɓuwa gami da faɗaɗa har zuwa wannan lokaci da ya shafe shekaru 10 cif. Fitaccen ɗan Jarida daga Najeriya Abdulbaqi Aliyu Jari shi ne ya jagoranci assasa wannan rana mai muhimmanci ga Harshen Hausa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman...............
Shirin al'adun gargajiya na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya yada zango ne a Ghana, inda a ‘yan kwanakin da suka gabata, ‘Yan Ƙabilar Zarma ko kuma Zabarmawa suka yi taron baja kolin al'adunsu karo na huɗu a ƙasar. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda zamani ke tasiri kan salon magana ko 'Gagara Gwari' a tsakanin al'ummar Hausawa, musamman ma matasa. Masana wannan harshe da dattawa cikin al'ummar sun yi fashin baki akan dalilan da suka sanya wannan salo na zance wanda ke nuna ƙwarewar harshe ke neman ɓacewa, da gudummawar da kowane ɓangare ke bayarwa wajen wannan matsalar.
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne aka wata al'adar al'umar Tangale dake jihar Gomben Najeriya wacce a shekara ke haɗo kan ɗaukacin al'uma na ciki da wajen ƙasar. A alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.
Shirin na wannan mako ya yi duba ne kan al'adar nan da ta jima tana cin kasuwa a ƙasar Hausa, wato Sallar cika ciki da ake gudanarwa bayan Sallar layya. Tsawon shekaru da wannan al’adar ta dore,ake kuma ci gaba da gudanar da ita a wurare da dama. Al'ummar Hausa da dama a birane da karkara a duk ranakun tara da goma ga watan farko na shekarar musulunci wato Muharram, sukan gudanar da azumin da kuma raya al'adar nan mai suna cika ciki wato dai sai kaci ka koshi kuma abinci mai dadi, wasu kan amfani da iya abinda suke da shi, yayinda wasu suke karawa da hidindimu. Wani abin lura shine, yadda a yankunan karkara, idan wannan lokaci ya ƙarato, jama’a musaman mata na dukufa ne ɓangaren girki, inda a wajen gida yara matasa kan ɗora sanwa wasu lokutan su kan yi amfani da haka wajen raya al’adar nan da aka sani da aci a cika ciki sannnan ga nishaɗi. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan guda cikin al'adun Ƙabilar Kanuri can a kudu maso gabashin Jamhuriyyar Nijar, Al'adar da ake yiwa laƙabi da ''Mai suna'', al'adar da ke da matuƙar tasiri a cikin wannan ƙabila da ke da matuƙar yawa a ƙasashen Najeriya da Nijar da kuma Kamaru. Al'adar ta Mai suna ko kuma takwara, na cikin al'adu masu matuƙar girma a wannan ƙabila da kuma ke da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ƴan uwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin al'adun mu na gado na wannan rana ya mayar da hankali kan gudunmowar marubuta wajen adana gargaji da tsrain al'adu Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa
Shirin al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya maida hankali a kan bikin al'adun Dukkawa na wanan shekara ta 2025 wanda ya gudana a jihar Neja da ke Tarayya Najeriya. Ku shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shiri.......
Shirin Al’adunmu na Gado a wannan karon ya tattauna ne a kan Maita da kuma Kambun Baka, domin fahimtar banbancinsu a bisa bayanan masana a ɓangaren al’ada da kuma Addini. Wasu na ɗaukar maita a matsayin tsubbu inda a lokuta da dama su kan gadar wa ƴaƴansu. Sai dai kuma wasu masanan, na cewa maita baiwa ce da Allah ya yi ma wasu daga cikin bayinsa musamman domin bayar da magani ga marasa lafiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman........
Wannan shiri zai mayar da hankali ne kan yadda zamani ke tasiri akan salon magana ko gagara gwari a tsakanin al'umar hausawa, musamman ma matasa masana da dattawa da suka jiya suka ga yau sun bayyana dalilai da suka sanya irin wannan salo na zance, wanda ke nuna ƙwarewar harshe ke neman ɓacewa a tsakanin al'uma da gudummawar da kowanne ɓangare ke bayarwa wajen disashewar wannan fiƙira ta harshe.
Shirin al'adun mu na Gado na wannan mako zai Dora kan ci gaban Muhawara a tsakanin Masana kan kwarewar waƙa a tsakanin mawaki Shata da kuma Rarara Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin, tare a Nasiru Sani
Shirin al’adu na wannan makon ya waiwayi al’adar waƙoƙin Hausa ne da kuma tasirin Mawaƙan da suke rera su waƙoƙin a fannonin rayuwa daban daban. A baya bayan nan aka tafka muhawara tsakanin wasu masana guda biyu na Adabin Hausa wato Dakta Abdul-Shakur Yusuf Ishaq na Jami’ar Jihar Kaduna da kuma Dakta Mu’azu Sa’adu Kudan na Jami’ar Sule Lamiɗo da ke Kafin Hausa a jihar Jigawa, waɗanda suka baje iliminsu a kan matakin shahara, da kamance-ceniya da kuma banbanci a tsakanin Marigayi Mamman Ibrahim Yero da aka fi sani da Mamman Shata ko kuma Shata mai Ganga da kuma Dauda Adamu Kahutu Rarara da a halin yanzu zamani ke tafiya da shi.
Shirin a wannan makon zai tattauna ne a kan Camfi, da kuma yadda ya kasance a zamanin kaka da kakanni, da rawar da ya taka a waccan lokaci da kuma yadda yake shafar rayuwar jama’a a lokacin da muke.Duk da ƙarancin lokaci, shirin Al’adunmu na gado zai yi ƙoƙarin zayyana rabe-raben al’adar ta Camfi ko kuma wasu daga ciki.



