DiscoverNajeriya a Yau
Najeriya a Yau
Claim Ownership

Najeriya a Yau

Author: Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Subscribed: 4Played: 61
Share

Description

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

564 Episodes
Reverse
Akwai abubuwan da ya kamata a rika bayyana wa mata idan za su yi aure amma kunya tana hanawa.Wasu sai sun je gidan aure suke tarar da abubuwan da ya kamata ace sun sani daga magabata, amma sai dai su tsinta a wajen kawayensu.Shirin Daga Laraba ya duba dalilan da ya sa ake kin bayyanawa mata wasu mahimman abubuwan da ya kamata su sani idan za su yi aure.
Dambarwa ta siyasa ci gaba da daukar hankali game da dakatar da shugaban jam’iyar APC na kasaAna ta takaddama da zargin juna tsakanin jam’iyyun siyasa musamman na Kano da gwamnati mai ci a can.Toh amma wa ke wasa da hankalin wani ko rura wutar rikicin dakatar da Ganduje a jam’iyar APC, Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani a kai.
Ba shakka dokokin kasa iri guda ne a duk inda ake a Najeriya.Sai dai ana yawan samun kotuna da yin mabambantan matsaya kan shari’a iri guda a lokuta daban-daban. Ko me ya jawo haka?Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa kotuna ke yanke hukunci daba-daban kan shari’a iri guda.
Ana ta murnar dalar Amurka na karyewa watakila a samu saukin kayan masarufi.Sai dai a ganin wasu yadda ‘yan kasuwa suke azamar tsawwala kudi idan ta tashi ba su yi hakan ba a yayin da take saukowa.Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilin da ya zama wajibi ‘yan Kasuwa su sauke farashin kayayyaki.
An shiga saƙe-saƙe game da mutanen da suka yi ikirarin dakatar da Ganduje daga jam’iyar APC tun daga matakin mazaba.Sai dai uwar jam’iyar ta yi watsi da hakan, inda kuma daga bisani suka zargi jami’iyar adawa.To amma ko da ace za a dauki irin wannan matakin, wa ke da hurumin dakatar da shugaban jamiyar APC na kasa a dokance? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani.
Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ya sa komai ya sauya amma banda albashin ma’aikata.Akwai mahimman abubuwan da masu daukar albashi ba su iya yi saboda ma’aikatu da hukumomi sun kasa matsawa da albashinsu gaba.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da ya kamata mutum ya fara dubawa ta fannin albashi kafin karbar aiki.
Wane lokaci ya fi dacewa mutum ya fara azumin sitta-shawwal?Ana yawan shiga rudani kan hakan, da kuma tunanin cewa mace wadda ake binta bashin azumin Ramadan ko ya kamata ta dauki azumin kafin biyan bashi?Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani da wasu batutuwan da ya kamata ku sani game da azumin na kwanaki shidan bayan karamar Sallah.
Matsin rayuwa yana daga cikin abin da ya hana mutane da dama yin shagali da wannan karamar Sallah.Wasu ma basu iya yin cefanen Sallah na abincin da za a ci ballantana sabbin dinkuna.Shirin Najeriya a Yau ya zagay wasu jihohu domin yadda mutane suka yi Sallah cikin matsin rayuwa.
Teloli iyayen haɗa gwarama! An saba kai ruwa rana a kowace Sallah idan teloli suka sha ta fi karfinsu.Sai dai ba saban ba, wani telan da muka zanta da shi ya ce ya kammala dinkunan da ya karba kakaf yayin da wani ya tsere ya bar masu kaya da wayyo!Shin wadanne dabaru ya kamata tela ya yi amfani da su wajen ganin ya sallami kowa? Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani.
Shin a wane lokaci aka yi umarnin fitar za Zakkar Fidda Kai?Malamai sun ce wannan Zakka tana da matukar mahimmanci ga masu hali kuma akwai lokacin da aka kayyade a fitar da ita; in ba haka ba kuma ta zama sadaka.Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan fidda Zakatul-Fitr da mutanen da aka haramtawa cin ta.
Tun bayan da aka kara kudin wutar lantarki mutane ke ta korafi game da yadda aka rarraba tsarin.Amma har yanzu wasu na cewa ba su fahimci yadda tsarin yake tafiya ba da kuma yadda lamarin ke neman shafar rayuwarsu matuƙa.Shirin Najeriya a Yau ya tattaun kan abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon tsarin rabon lantarkin.
Akwai abubuwa na musamman da aka fi son a roƙa a irin wannan dare.Yawanci an fi maida hankali a ranakun wutiri daga 25 zuwa 29, duk da yake malamai na ba da shawarar a yi ibada sosai a dukkanin ranakun goman karshe.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da malamai gameda alamomin gane daren lailatul-ƙadri da abin da aka fi son bawa ya roƙa a ciki.
Yanayin tsaro na jefa fargaba a zukatan wasu Musulmi da ke zuwa sallar dare ta Tahajjud.Wasu ɓata gari kan yi amfani da wannan damar da mutane ke fita tsakar dare domin aikata musu abin da bai dace ba.Shirin Najeriya a Yau ya duba wasu matakai na tsaro da za ku dauka domin kare kanku daga fadawa matsala.
Shin a ganinku me ya sa matasa 'yan soshiyal midiya suka dukufa a harkar nan ta kirifto musamman 'mining' ?A yanzu haka da dama ne cikin matasan ke jiran ta fashe domin su kudance, sai dai akwai masu yi wa irin wadannan matasa kallon masu raunin zuciya.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da masu harkar mining da kuma masana kirifto kan abin da ya kamata ku sani kafin ku fara hakowa.
Yawan amfani da Soshiyal Midiya na haifar da gane-ganen abubuwan da ba su kamata ba.A lokacin Ramadaan yana da kyau mutum ya yi kokarin kaucewa duk wani abin da zai raunana mishi azumi.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da zai faru da ku idan kuka yawaita amfani a da soshiyal midiya a lokacin Ramadan.
Mutum sama da 300 aka saki ga gwamnatin jihar Borno a satin nan bayan wanke su daga zargin kungiyar Boko Haram.An dade ana tsare da su tsawon shekaru amma sai yanzu aka gano ba su da hannu. To amma me dokar kasa tace game da irin wannan tuhuma bayan an gano gaskiya?Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan halin da aka jefa su da kuma yadda doka za ta yi musu adalci.
Za a  iya cewa aikin Hajji a Najeriya sai ga mai rabo, domin tun bayan bullar labarin hukumar alhazan Najeriya NAHCON na cewa an yi ɗori kan kudin da aka ware a baya ake ta ƙorafi.Tuni wasu maniyyatan suka ce sun cire rai a yanzu, amma kuma hukumar ta ce akwai dalilan da babu yadda ta iya da su ne.Shirin Najeriya a Yau ya duba matakin, da wasu suka ce yana neman hana talakan Najeriya zuwa aikin Hajji.
An shafe tsawon wunin jiya Lahadi ana  zaman jira da dakon isowar daliban Kuriga da gwamnatin jihar Kaduna tace ta ceto.Saidai daga bisani, ba tare da wani cikakken bayani ba an umarci iyayen yaran su sake dawowa a yau Litinin domin amsar ‘ya’yan nasu.Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa gwamnatin ta dauki wannan mataki ba tare da wani cikakken bayani ba.
Fannin shari'a musamman alkalai a matakin tarayya sun samu kari kan albashinsu na baya.Ana ganin hakan zai samar da sauyi ga fannin shari'a da kuma dakile cin hanci ta wasu fannin, ko da yake wasu na ganin ba abin da ake bukata a fannin a yanzu ba kenan.Shirin Najeriya a Yau ya duba sauyin da karin albashin zai iya haifarwa a kasar.
loading
Comments 
loading
Download from Google Play
Download from App Store