Discover
Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Author: Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim
Subscribed: 2Played: 59Subscribe
Share
© 2023 Najeriya a Yau
Description
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
486 Episodes
Reverse
Rubutun kundin kammala karatu da ake kira da “project” daya ne daga cikin abin da ke dagula lissafin dalibai a makarantun gaba da sakadire. Mene ne gaskiyar abin da ake bukata a “project”? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe cikakken bayani kan abin da ake bukata a rubutu.
A Jiya Alhamis cikin shirin Najeriya A Yau mun dubi yadda da zarar an ga shekaru sun dan fara ja ana sa ran a cimma wani buri na rayuwa da zai sa a ga cewa mutum ya fara samun cigaba da zama cikakken mutum. Mun yi amfani da shekaru 30. Shin ka saurari wannan shirin da ya yi magana kan Matakin Da Ya Kamata Matashi Ya Kai Kafin Ya Cika Shekara 30? A yau shirin na tafe da shawarwarin mafita ga wadanda su ka wuce shekaru 30 amma babu kwakkarar madafa.
Shin kun taba tambayar kanku matsayin da ya kamata matashin da bai wuce shekara 30 ya taka?Da zarar shekaru sun ja ana sa ran a cimma wani buri na rayuwa da zai sa a kalli cewa mutum ya fara samun cigaba da zama cikakken mutum.Shirin Najeriya a Yau ya duba matakin da ya kamata a ce mutum ya kai kafin cika shekara talatin a rayuwa.
Ana ta kai ruwa rana a majalisar jihar Filato gameda yadda shugabanci zai kasance daga ɗan jam'iyar adawa da ba su da rinjaye.Akwai 'yan majalisar APC da kotu ta baiwa nasara bayan tsige mafi yawancin yan jam'iyar PDP, duk da yake ba a rantsar da su ba amma majalisa tana hutu.Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake tirka-tirka a majalisar dokokin jihar Filato da zargin barazanar tsige kakakinta.
Jama’a na yi wa zazzabin malariya kallon wani zazzabi da bai taka kara ya karya ba. Sai dai kuma masana suna yiwa wannan zazzabi wani irin kallo. Ko kun san manyan cutukan da zazzabin malariya zai iya haifarwa? Shirin namu na wannan lokaci na tafe da gamsassun bayanai kan hanyoyin kariya.
Ýan damfara kullum na kara kaimu wurin fito da sabbin dabarun cutar jamaá ta hanyoyi daban daban. Shin ko kun san ana iya tura maka alat da rasit din kudi na bogi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da wadansu da aka turawa rasit da alat na bogi, ya kuma ji ta bakin wani masani kuma mai sharhi akan dabarun sadarwa ta intanet.
Lamarin ya kai da wuya mutum ya fito ya koma gida ba tare da wani ya yi masa ba-zata ya roke shi kudi ko abin ci ba.Yawancin masu irin wannan rokon sukan fito ne tsaf-tsaf kamar wasu ma’aikata ko ’yan kasuwa.Shin yaya jama’a ke kallon wannan dabi’a da ta zama ruwan dare?Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci na tafe da karin bayani.
Rayuwa ta kan sauya a duk lokacin da mutumin da ke zaman waƙafi a gidan kaso ya shafe dogon lokaci babu hukunci amma daga bisani aka sake shi.Akwai dubban mutane da ke jiran yanke hukunci a kotuna da kuma waɗanda basu san makomar su ba.To amma me ya sa ake samun wannan tsaiko? Abin da shirin Najeriya na yau ya duba kenan.
Lokaci daya ne daga cikin abubbuwan da ake wasa dasu masu matukar muhimmamnci a Najeriya. Wanda sakamakon hakan mutane na tafka asara. Shin Mene ne abin da yasa ‘yan Najeriya ke wasa da lokaci? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu da idon basira.
Tun dauri a arewacin Naijeriya, Maza aka sani da rike da ragamar gida, ta hanyar fita a nemo abun da za a ciyar da iyali, yayin da mata ke lura da aikace-aikacen gida.Wasu matan kan yi sana’o’i na gida da niyyar samun kudin kashewa da ba dole sai an tambayi maigida ba.To a yanzu an shiga yanayin da wasu mazan ke sakarwa mata ragamar gida kacokan. Shirin Naijeriya A Yau, ya yi duba ne kan wannan ta’ada ta wasu mazajen, da yadda matan ke fama wajen daukar nauyin gida.
Da zarar an shiga lokacin sanyi, a kan samu cututtuka da dama dake yawo saboda kaɗawar iska.A gefe guda kuma akwai batun kula da lafiyar fata ga masu kaushin jiki da bushewar fata.Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan da ya kamata ku dauka wajen kare lafiyar ku a lokacin sanyi da hunturu.
Kotuna da dama sun yanke hukunci mabanbanta a kan kujerun gwamnoni, inda aka soke wasu da suke jam'iyyar adawa da ma jam'iya mai ci.Ana ganin hakan kamar wani sauyi ne ga dimokraɗiyya wajen yanke hukunci ba sani ba sabo.Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan ci gaban da aka samu ga dimokraɗiyya bayan hukunce-hukuncen kotuna kan kujerun gwamnoni.
Raye-raye da tsalle-tsalle na rashin tarbiyya na ci gaba da samun karbuwa a kafar sada zumunta na zamani da ake wa lakabi da Tiktok. Ta yadda kusan babu irin rashin tarbiyyar da ba a bayyanawa a wannan kafa. Shin wace irin illa wannan kafa take yi ga cigaban karatun matasan Najeriya?
Buhun albasa a kasuwannin Arewacin Najeriya ya kai sama da Naira Dubu Dari a ýan kwanakin nan. Shin mene ne abin da ya sa albasa tsada fiye da sauran shekaru a Najeriya? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da manoma, manyan ýankasuwar albasa da kuma wata likitar abinci akan tsadar albasa da amfaninta a jikin dan Adam.
Yajin aikin 'yan ƙwadago ya haɗa har da na malaman jami'o'i a Najeriya, inda aka kulle makarantu a matakai daban-daban.Hakan yana shafar ɓangaren ilimi da wasu ke ganin za a samu koma baya idan ba a dakatar da yajin aikin ba.Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan tasirin yajin aiki ga fannin ilimi ko akasin haka.
Mutane da dama kan ce wani magani ya daina yi musu aiki ko kuma baya yi musu aiki bayan a wani lokaci da ya wuce yana yi musu aiki. Mene ne abin da ke hana magani aiki a jikin mutum? Shirin namu na wannan lokaci na tafe da tattaunawa ta musamman akan abin da ke hana magani yin aiki a jikin dan-Adam.
Sayen kuri’a daya ne daga cikin abubbuwan da masana ke bayyanawa a matsayin wani abu da ke tadiye kafar Dimukuradiyya a Najeriya. Mene ne abin da ya kamata a yi domin hana sayen kuri’a? Shirin Najeriya A Yau ya dubi yadda ake sayen kuri’a a zabukan Najeriya, ya kuma tattauna da masana kan hanyoyin da za a bi domin magance wannan matsala.
Wahalar tsabar kudi na cigaba da karuwa a wadansu jihohin Najeriya duk da bayanin cigaba da amfani da tsoffin kudaden da CBN ya ce a ci-gaba da yi. Idan ba a manta ba, a watan Mayun wannan shekarar kotun kolin Najeriya ta ce a cigaba da amfani da tsoffin kudaden har 31 ga Disamba mai zuwa, sai kuma gashi CBN ta fitar da sanarwa kafin wannan lokaci, duk da cewa sanarwar ta CBN ba ta ci karo da umarnin kotu ba, zuwa yaushe CBN ke nufi, kuma mene ne abin da doka tace danagane da batun na CBN. Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan
Farashin Gas din girki yana ta hawa da sauka a kasuwanni daban-daban, lamarin da ya sa iyalai da dama ke kukan yadda hakan ke tilasta su ajiye amfani da tukunyar Gas.Wasu diloli na cewa abin da ke faruwa ba laifinsu bane, yayinda magidanta ke ganin ba yadda suka iya yanzu tunda sun saba da yin girki da Gas.Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda hauhawar farashin Gas ya tilastawa magidanta konawa amfani da itace da gawayi wajen girki.
Ana murna da raguwar hare-haren 'yan ta'adda a yankin Arewa maso gabas, sai ga shi wasu alamu na nuna akwai yiwuwar wasu na shirin dawo da hannun agogo baya.A 'yan kwanakin nan an samu barazanar kai hare-hare da wasu bayanan sirri a yankunan da ake ganin an ci ƙarfin 'yan ta'addan.Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda 'yan ta'adda ke yunƙurin dawo da kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya.