DiscoverDaga Laraba
Daga Laraba
Claim Ownership

Daga Laraba

Author: Aminiya

Subscribed: 2Played: 24
Share

Description

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
152 Episodes
Reverse
Bayan komawa tsarin rukuni daban-daban na bayar da wutar lantarki Idan kamfanoni na neman afuwa to yawancin ga ‘yan rukunin farko ne.Wasu na ji a ransu kamar su ba kwastomomi bane ga kamfanonin domin kulawar da ake ba su ta nuna ba a tare da su.Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa hankalin kamfanonin wutar lantarki ya karkata wani fanni.
A watan Ramadan sabbin ma'aurata na alfahari da azuminsu na farko a gidan aure.Shin mene ne abin da yake kayatar da gidan aure musamman a wannan lokaci na Ramadan? Ya ya kamata ma'aurata su kasance?Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna yadda ma'aurata ke samun tabarruki da falala a yanayinsu na farko.
I’itikafi  sunna ce mai karfi a wannan lokaci, kuma jama’a masu sukunin shiga na kwashe kwanaki kusan goma a masallaci wajen ibada.To amma me ya kamata ku sani gameda shiga itikafi kuma wadanne abubuwa ake son mutum ya kiyaye a lokacin?Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba matakan yin i'itikafi da abubuwan da ya kamata ku sani gameda hakan.
A yayin da ake shiga goman tsakiya na watan Ramadan, malamai na kira ga al’umma da su dage wajen ibadu domin samun dacewa.A al’adance a wannan goma ta tsakiya akwai wasu al’adu musamman na tashe da kuma kirarin goma ta wuya bayan ta marmari.Shirin Daga Laraba ya yi tsokaci ne a kan wasu abubuwa da da ake yi a goman tsakiyar Ramadan a addinance da al'adance.
Watan ramadana na jefa shauki a zukatun yara masu tasowa ta yadda har rige-rige ake tsakanin juna na ganin an kai wannan munzali.Shin ta wace hanya ya kamata iyaye su bi domin koya wa yarasu azumin ramadana?Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan koyawa yara azumin ramadana cikin sauki.
Mutane da dama sun shaida cewa takardar Nairar Najeriya na saurin lalacewa.Wasu na ganin masu liki a wajen bukukuwa da yadda ake kasuwancin sabbin kudi na taka rawa. Toh amma me ya kamata a yi, me kuma doka tace kan kudin da suka tsufa suka lalace.Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba halin da mutum zai iya jefa kansa idan har aka same shi da wulakanta takardun Naira da yadda za a bada gudummuwa wajen inganta kudin.
Tsadar rayuwa ta sa ruwan leda wato 'fiyowata' ya fara zama abin tattaunawa gameda yadda yake tsada.Wasu na ganin shine ruwan da ake samu mai dama-dama wajen tsafta idan mutum na so ya sha ruwa, sai dai yadda yake kara tsada a sassa daban-daban na Najeriya ya sa ana komawa shan  ruwa mara tsafta a wasu wuraren.Sai dai masu sarrafa ruwan na cewa ba daga su ba ne, inda har ta kai ga wasu na rufe kamfanoninsu.Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dalilin da suka jawo hakan.
Wannan rana ce majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar harshen uwa ta duniya. Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 40 cikin 100 na al’ummar duniya ba sa samun ingantaccen ilimi ne saboda rashin amfani da yarukansu na asali.Wasu harsuna na fuskantar barazanar shafewa a duniya saboda iyaye sun daina koyar da ’ya’yansu yadda za su yi magana da harshen. Shirin Daga Laraba na dauke da karin bayani.
Ranar masoya kan dauki hankali a ranar 14 ga watan Fabreru, inda yawancin masoya ke kure malejin soyayyarsu.Amma akwai masu ganin ba lallai a samu soyayyar gasakiyaa yanzu ba. Sai dai ko kun san yadda aka yi wannan ta samo asali?Albarkacin ranar masoya Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba tasirin wannan rana da salsalar ta.
Kafafen sada zumunta sun zama farfajiyar baje kolin basira, yayin da ta kan zame musu hanyar bayyana damuwa da share kokensu. Ana yawan buga misali da cewa an yiwa yankin Arewacin Najeriya  nisa wajen samun tagomashin a soshiyal midiya.Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dabarun da masu amfani da shafukan za su bi wajen  ganin sun amfana yadda ya kamata.
A duk lokacin da ma’aikaci ya tsinci kanshi a ofishi mai matsin lamba da takura, masu sharhi na ganin aiki bai cika tafiya daidai ba.Wasu wuraren aiki na fuskantar matsin lamba daga oganni ko kuma tsarin aiki da zai sa a yi ta korafi.Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba yadda wuraren aiki masu matsin lamba ke takura rayuwar ma’aikata da yadda za a warware damuwa a irin wannan yanayi.
Lafiya dai ita ce uwar jiki, babu mai fushi da ita. A yanayin da aka ciki babu mai son ya ga ya kwanta rashin lafiya, domin ana lallaba halin da ake ciki.Jama’a na kokawa a fannoni da dama yayinda wasu kyale batun ziyartar asibiti ko shan magani ko da sun ji alamar canji a jikinsu.Ku kasance da shirin Daga Laraba na wannan mako domin wasu dabarun da za su taimaka wajen ganin ba ku kwanta rashin lafiya ba.
Abu ne da za a iya cewa sananne ga al’ummar Kano da Zazzau na tsokanar juna a tsakaninsu.Ana yawan taƙaddama kan shin wane ne mai gida tsakanin Kanawa da Zazzagawa.A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako mun duba tasirin wannan wasa tsakaninsu da kuma yadda ta samo asali.
Rade-radin matsaloli basa karewa dangane da masanaantar shirya finafinai ta Arewacin Najeriya mai cibiya a Kano Kannywood. Shin mene ne abin da ke hana Kannywood cigaba kamar sauran takwarorinta na duniya? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi boyayyun matsalolin da suka dabaibaye Kannywood. 
Yanzu wata guda kenan tun bayan da sojoji suka yi kuskuren kai hari kan masu Maulidi a garin Tudun Biri dake jihar Kaduna.Harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 100, inda hukumomi da gwamnati ba su yi wata-wata ba wajen daukar alhakin hakan da kuma bayyana cewa za a yi abin da ya dace wajen bin hakkin waɗanda lamarin ya shafa.Toh shin zuwa yanzu wane hali ake ciki? Ko an fara bincike kuwa? Ina kudaden da aka tara na tallafi suke?Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazari na musamman a kan matakin da ake kai na bincike kan harin.
Tasirin goro ga masu cinsa yana zama abu mai wahala mutum iya dainawa. Goro na da mahimmanci a Kudancin Najeriya musamman ga Kabilar Igbo.Haka ma yawanci dattawa a Arewacin Najeriya har ma matasa da mata a wasu lokutan suna cin goro, inda abin ya kan zame musu jiki, yayinda ake amfani da shi a wajen taruka na aure ko suna duk da ba a nomanshi a yankin.Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba abin da ya sa masu cin goro basu iya dainawa da kuma abin da masana suka ce zai iya faruwa idan cinsa yayi yawa.
Da zarar an ambaci wasiyya sai mutum ya fara tunanin mutuwa, ko wani abun na daban a rai.Wasu kan bar wasiyya ko da za su yi tafiya zuwa anguwa saboda gudun riskar wa'adi a lokacin da ba shiri. Shin ya mahimmancin wasiyya take da kuma tasirin hakan?Ku biyo mu shirin Daga Laraba na wannan makon domin jin mahimmancin barin wasiyya tun mutum na raye.
Maza da dama na son aure amma kuma su kan ce fargabar ɗawainiya ta hana su. Wasu kuma na cin karo da ƙalubale tun a wajen nema, lamarin da ya sa suke zarta shekarun samartakansu  ba aure. Toh shin da gaske ne abinda suke fada na cin karo da kalubale bayan aureKu biyo mu cikin shirin Daga Laraba na wannan makon inda muka duba yadda wasu mazan kan shafe sama da shekara 40 ba aure.
Shin kun yarda cewa garin kwaki na kashe ido ko zuƙe ruwan jiki?Wasu na shan gari a matsayin abinci su koshi, yayinda wasu ke sha dan marmari.A cikin shirin Daga Laraba na wannan makon mun duba gaskiyar zancen cewa garin kwaki yana kashe lafiyar ido ko akasin haka.
Mutune kan  ziyarci asibiti domin gwaji inda a wasu lokutan ake bayyana musu cewa suna da karancin suga a jikinsu.Akwai alamomin da masana ke cewa su ke nuna mutum na da karancin suga a jiki, amma kuma akwain abubuwan da ke haddasa hakan.Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba yadda za ku gane kuna da karancin suga a jikinku da kuma matakan kariya.
loading
Comments 
Download from Google Play
Download from App Store