DiscoverDaga Laraba
Daga Laraba
Claim Ownership

Daga Laraba

Author: Aminiya

Subscribed: 1Played: 24
Share

Description

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
97 Episodes
Reverse
Ana sa ran a tashi da Azumin watan Ramadan mai albarka ranar Alhamis idan Allah ya yarda. Shin kun san matakan samun nasara a cikin ibadar wannan wata? Shirin Daga Laraba na wannan karo ya tattaro bayanai da shawarwari na alheri game da yadda za a rabauta da alheran da ke cikin watan azumin Ramadan. 
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya leka banki da kasuwa kuma ya gano yadda jama’a ke fama da rashin kudi, ga shi kuma wasu ’yan kasuwa sam ba sa karbar tsohuwar Naira, sai sabuwa ko taransfa.Ko yaushe za’a sakar wa ’yan Najeriya Naira?Saurari Daga Laraba domin jin amsar wannan tambaya, dama wadansu masu alaka.Za ku so karanta wadannan
Shirin Daga Laraba na wannan karo ya yi wasu tambayoyi masu kalubale ga shugaban kasar Najeriya mai jiran gado game da lafiyarsa, da kuma kaifin basirarsa.Shin Bola Ahmed Tinubu zai iya tafiyar da harkokin mulkin Najeriya fiye da Muhamadu Buhari?Ku surari shirin Daga Laraba na wannan mako ku ji amsoshin duka tambayoyin namu.
Ku biyo shirin Daga Laraba na wannan karo ku ji yadda sakamakon zaben shugaban kasa da ’yan  majalisun tarayya na shekarar 2023 ya zo da sabon salon da watakila ba a taba ganin irinsa a wannan zamanin ba.A cikin shirin, za ku ji yadda gwamnoni masu ci suka sha kasa a yunkurinsu na zuwa Majalisar Dattawa.  
Ranar Asabar 25 ga Watan Fabrairun da muke ciki ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayyar Najeriya.Shin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shirya gudanar da wannan gagarumin aiki?Shirin Daga Laraba ya leka lungu da sako a Najeriya domin sanin matakin shirin hukumar zaben da kai.
Nan da kwana tara ’yan Najeriya za su zabi sabon shugaban da zai mulke su na tsawon shekaru hudu idan Allah ya yarda.Bisa la’akari da yadda yakin neman zabe ke gudana, wane ne cikin ’yan takarar ke da alamun nasara a zaben na mako mai zuwa? Shirin Daga Laraba ya tattauna da kwamitin yakin neman zaben manyan ’yan takarar da ake sa ran daya daga cikinsu zai zamaz zababben shugaban kasar Najeriya, inda kowannensu ya bayyana yadda yake kallon nasara da kuma kalubalen da ke gabansu. A yi sauraro lafiya. 
Sabuwar dabi’ar neman miji ta kafofin sada zumunta da ’yan mata ke yi na neman zama ruwan dare.Bisa al’adar bahaushe dai, namiji ne ke ganin mace ya ce yana so; To amma sai ga shi ’yan mata sun dukufa tallata kansu ga mai so a kafofin sada zumunta. Shin me ke faruw ne? Shirin Daga Laraba ya tattauna da wasu ’yan mata kan abin da ke sa su dora hotunansu a kafofin sada zumunta don neman miji; mun kuma ji ta bakin samari kan yadda suke kallon matan da ke yin hakan. 
A farko babu wanda ke yarda yana dan taba karya lokaci bayan lokaci. Amma idan aka dan matsa da bincike sai a samu jama’a da dama na dan tabawa.Ko mene ne ya sa mutane ke yin karya? Shirin Daga Laraba ya tattauna da wadansu da suka yarda suna yin karya, sun fadi dalilansu, mun kuma ji ta bakin masana kan dalilin yin karya da kuma hukuncinta. 
Matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa ta tilasta wa 'yan Najeriya sauya yadda suke rayuwa. Shin kun san irin halin da jama'a ke ciki, kawo yanzu? Shirin Daga Laraba ya binciko hakikanin halin da ake ciki, ya kuma tuntubi dalilai.  
Batun alaka tsakanin ’yan aiki da iyayen gidansu ya jima yana daukar hankali a fagen musayar ra'ayi. Shin tsakanin ’yan aikin da masu daukarsu, wa ke da alhakin abin da ke faruwa?Shirin Daga Laraba ya kutsa lungu da sako, ya zakulo ’yan aiki ya kuma ji ta bakin masu daukar aikin. 
Muhawara kan abin da ke sa maza tsoron matan da suka yi karatun boko mai zurfi ko masu dukiya, batu ne da ya jima yana daukar hankalin jama’a da dama. Shin ko matan da suka yi karatun boko mai zurfi sun san dalilan da maza ke tsoronsu? Shirin Daga Laraba ya binciko wadan nan dalilai, ya kuma baje su a gadon fida, inda masana suka fede biri har wutsiya. 
A kwankin baya mun kawo muku shiri na musamman akan yadda ake aure da ciki a wannan zamani.Wannan karon, shirin ya dubi yadda yaudara ta zamo ruwan dare a tsakanin masu shirin aure.Shin kunsan yadda yaudara ta zamo rigar ado a wannan zamani?Shirin Daga Laraba na tafe da bayanai masu ratsa zuciya, da kuma mafita kan yaudara a fagen soyayya. 
Zumunci wani jigo ne a tsarin rayuwar malam Bahaushe a shekarun baya, amma yanzu yana neman zama tarihi.Shin yaya aka yi yanzu zumunci ke neman zama labari a tsakanin al’umma?Shirin Daga Laraba na kunshe da bayanai. A yi sauraro lafiya.
Shin idan ka gano cewa da cikin wani amaryarka ta shigo gidanka wane mataki za ka dauka?Shirin Daga Laraba na wannan mako ya bankado al’ada yin aure da juna biyu a Arewacin Najeriya.Shin da sanin angwaye ake daura musu aure da mata masu ciki?Gyara zama domin jin yadda ta kaya tsakanin wadansu angwaye da amarensu suka zo musu da cikin wasu.
Matsalar yawon talla ta dade tana ci wa al’ummar Arewacin Najeriya tuwo a kwarya.Me ya sa aka fi dora wa ’yan mata talla ta kasar Hausa kuma tsakanin amfani da illolin talla wanne ne a gaba?Shirin Daga Laraba ya dubi maganar talla da idon basira, don neman mafita ta hanyar tattaunawa da hukumomi da masana a fannin ilimin addini da na duniya.
Shin me ya sa kayayyaki marasa inganci suka zama ruwan dare a Najeriya?Wani lokacin kayayyaki na jabu ko lalatattu da ake sarrafawa ko sayar wa ’yan Najeriya na hallaka da dama a cikinsu.Me hukumar da ke kula da ingancin kayayyaki ke yi don hana kawo wa ’yan Najeriya kayayyaki marasa inganci?Saurari shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin wainar da ake toyawa.
Zubar da ciki al'amari ne mai ba da tsoro saboda hadarinsa da kuma alhakin da ake iya dauka idan an yi ba bisa ka’ida ba.Shin ko mene ne dalilin da zubar da ciki ya zama ruwan dare a tsakani ’yan mata da matan aure a Najeriya? Saurari cikakken shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin yadda matan aure da ’yan mata suka maida zubar da ciki abin wasa.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya mayar da hankali ne a kan maganin karfin maza, amfaninsa, illolinsa da kuma shawarwarin masana a kai.Wannan kari ne a kan shiri na musamman da muka kawo muku a baya kan maganin mata, wanad aka fi sani da kayan mata da yadda ya samu karbuwa a tsakanin mata musamman a Arewacin Najeriya.
Shirin Daga Laraba na wannan lokaci ya dubi yadda matsalar lalata tsakanin iyaye da ’ya’yansu ko tsakanin yayyu da kanne ta zama ruwan dare ne.Mun tattaro bayanai masu nuna yadda kwamacalar take kara kamari a wannan zamani.
Me ya sa ake yawan samun mutane masu manyan shekaru da ke afka wa kananan yara mata ko mazayarinya ko karamin yaro?Shin wane dalili ke sa kawo yawaitar wannan kazamar dabi’a ta lalata da kananan yara?Shirin Daga Laraba ya dubi yadda wannan matsala ta zama ruwan dare, musamman a Arewacin Najeriya.A yi sauraro lafiya.
loading
Comments 
Download from Google Play
Download from App Store