DiscoverBirbishin Rikici
Birbishin Rikici
Claim Ownership

Birbishin Rikici

Author: HumAngle

Subscribed: 0Played: 0
Share

Description

Kokarin nutsawa cikin wahalhalun da mutanen da ke zaune a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula ke fuskanta, yawanci yakan zo ne kawai ta fuskar kididdiga; Birbishin Rikici wani shiri ne na mako-mako akan waɗannan labarun sirri na wadanda rikici da tashin hankali suka shafa da HumAngle ke kawo muku.

102 Episodes
Reverse
A ranar 25 ga Fabrairu shekarar 2014, 'yan ta'addar Boko Haram sun kai hari a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Buni Yadi a Arewa maso Gabashin Najeriya. Sun kashe akalla ’yan makaranta matasa 29 a lokacin da suke kwana a dakunan kwanansu tare da kona dukkan gine-gine tun daga dakunan kwanan dalibai har zuwa ajujuwa. Sai masallacin ya tsira. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Hauwa Shaffi NuhuMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
 A lokacin da ake fama da hare-haren Boko Haram a Najeriya, an samu asarar rayuka da dama. Binciken HumAngle ya gano cewa ana jibge gawarwaki da dama da ba a san ko su waye ba a asibitin kwararru na jihar Borno. Kusa da asibitin al’ummar Hausari ne, kuma suna da koke-kokensu. Muryoyin Shiri: Akila Jibrin, Samir Sherrif, Aliyu DahiruFassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Rashin Matsuguni

Rashin Matsuguni

2024-03-0905:02

 Wani magidanci mai suna David Jafaru mai shekaru 35 yana zaune ne a Kaduna, yana sana’ar tuka babur ne a lokacin da ya yi hatsari ya karya kafarsa. Hakan ya tilasta masa komawa gida a garin Dogon Noma don jinya. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Akila JibrinFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Maryam Adam, mace mai tsananin rashin son kai ta dauki matsayin uwa da uba tun tana karama.An tilasta mata zama uwa tana da shekaru 13, an tilasta mata barin makaranta, ta gudu daga tashin hankali, kuma ta koma gudun hijira. Da duk abin da ta shiga, ta kuduri aniyar baiwa 'ya'yanta rayuwa mai inganci.Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Kwanaki 105 Bilyaminu yana hannun masu garkuwa da mutane. A lokacin, iyalinsa sun yi duk abin da za su iya don tara kudin fansa da suka nema, ciki har da sanya gidajensu da gonakinsu don sayarwa. Amma hakan ya kasance da wahala sosai saboda manufar sake fasalin Naira ta Najeriya a wancan lokacin. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Akila JibrinFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
 Wannan shiri na #BirbishinRikici ya koma ne a lokacin da Najeriya ke fama da matsalar kudi inda a wani yunkuri na dakile tallafin ayyukan ta'addanci, babban bankin Najeriya ya bullo da sabbin tsare-tsare. Muna nazarin nasarorin manufofin yayin da wadanda suka tsira kamar Maimuna suka kwashe kwanaki a tsare har sai an biya kudin fansa. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
 Salamatu Buhari, mai shekaru 20, tana aiki a gonarta, tana da juna biyu, a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye kauyensu. Sai suka fara kashe mazaje suna yiwa mata fyade, ta ji sai ta ruga don ta kare kanta. A tsakiyar daji ta shiga naƙuda. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Zubaida Baba IbrahimMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
 An sace Lilian Daniel, ‘yar shekara 20 daliba a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2020 a lokacin da take komawa makaranta daga Jos a arewa ta tsakiyar Najeriya. Har yau babu wata magana kai tsaye daga gare ta. Wasiƙar baƙin ciki ɗaya kaɗai daga bauta. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Hauwa Shaffi NuhuMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Gudun Tsira

Gudun Tsira

2023-10-2803:05

Labarin Jummai da aka yi garkuwa da ita ya nuna wa daruruwan wasu mata da ake sacewa daga gidajensu, dakunan kwanan su, filayen gonaki, ko kuma lokacin da suke tafiya a yankuna da dama na arewa maso gabas. Saurari labarin juriya da jarumtaka da tayi akan wadanda sukayi garkuwa da ita.Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuci: Ahmad SalkidaMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Wata Rayuwa!

Wata Rayuwa!

2023-10-2205:56

Ahmadu Aga ya tuna rayuwarsa a baya a garin Boboshe, al’ummar da ke tsakiyar Borno da shauki.Yana daya daga cikin sama da mutane miliyan biyu da aka tilastawa barin garuruwansu zuwa wuraren da suka fi  tsaro a Najeriya da kasashen makwabta na Chadi, Nijar da Kamaru.Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuci: Murtala AbdullahiMuryoyin Shiri: Akila JibrinFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Aminu manomi ne a Daki Takwas, wani gari da ke Arewacin Najeriya. Amma ya kasa zuwa gonarsa saboda yawaitar sace mutane da ake da yaki karewa. Don haka rayuwa ta yi masa tsauri. Mun bibibiyi labarin Aminu, wanda dalibi ne da ya dogara da aikin gona don biyan kudin makaranta. Anma wuyar aikin a yanzu saboda tashin hankali ta janyo masa abin da ba zai manta ba. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Aisha Tijjani JiddaMuryoyin Shiri: Sameer SherrifFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Wataƙila mutanen da suka rasa matsugunansu sun riga sun yi asara mai yawa saboda tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, ‘yan uwansu, gidajensu, rayuwarsu, hankalinsu… Ta hanyar abubuwan da Hauwa, 14, da Adama, 22, za mu ga yadda yake da wuya a sami adalci ga wadanda aka yi wa fyade da kuma yadda rayuwarsu ta canza ba tare da jin dadi ba bayan cin zarafi.Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Aisha Tijjani JiddaMuryoyin Shiri: Khadija Gidado, Sabiqah Abdul-Ghaniy, Hauwa Abubakar SalehFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Kusan shekaru goma ke nan da Hauwa ta bar garinsu na Gwoza, har zuwa yau ta kasance ‘yar gudun hijirar da ke fuskantar kuncin rayuwa da ba za ta iya jurewa ba a babban birnin tarayyar Najeriya.Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
A wannan jerin da yake kunshe da labaran kisan Kiyashi na Buni Yadi,  za mu ji daga bakin wani ma’aikaci akan halin da aka shiga kafin a kawo harin da kuma bayan harin. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Hauwa Shafii NuhuFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
A wannan labarin na kisan kiyashin da aka yi a Buni Yadi, za mu ji daga bakin daya daga cikin yan matan wadanda yan ta'addan ba su yi musu komai ba. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuci: Hauwa Shafii NuhuMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Gibin da bacewar mutane ya samar a Arewa Maso Gabashin Najeriya ba karami ba ne. Wadansu giɓɓan manya ne da suka shanye mutane da yawa kuma suka jefasu rayuwar kunci. Saurari muryoyin yan uwan wadanda suka bata da kuma radadin da suke ciki. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuci: Kunle AdebajoMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Ranar Fargaba

Ranar Fargaba

2023-08-2605:51

Mansura Zubairu, Naja'atu Muhammad, da Khadijat Aminu na daga cikin daliban da suka yi sa'a. Da kyar suka tsallake rijiya da baya a lokacin da 'yan ta'adda suka kai hari a Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) a Birnin Yauri, a watan Yunin 2021. Har yanzu  suna tunawa da ranar ta'addanci da ba a saba gani ba.Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Khadija Gidado, Hauwa Saleh, Sabiqah Abdul-GhaniyFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
A shekarar 2014, Furaira da danginta sun gudu daga gidansu da ke Gwoza a Arewa maso Gabashin Najeriya zuwa Girei da ke makwabtaka da Adamawa. Bayan shekara guda ta daidaita da sabon yanayi, mijinta ya yanke shawarar yin ƙaura don ya sami aiki mai kyau. Amma yau shekara bakwai kenan bai dawo ba ko aika tallafin kudi ba.Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuciya: Rukayya SaeedMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Daga Gona Zuwa Kurkuku

Daga Gona Zuwa Kurkuku

2023-07-2203:30

Yeri Kambari, mai shekaru 40, ya bace ne a shekarar 2014 bayan da jami’an rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force (CJTF) suka kama shi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Bai shiga kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ba. Babu wani abu da ke nuna ya cutar da kowa. Ya tafi gona ne kawai kuma ya kasance abin ya shafe shi. Ya Kodo Alli, yayarsa, ta tuna abubuwan da suka faru kamar sun faru kwanan nan. Mai Gabatarwa: Rukayya SaeedMarubuci: Kunle AdebajoMuryoyin Shiri: Usman Abba Zanna, Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
Neman Tsira

Neman Tsira

2023-07-1503:39

Ga mutanen da suka rasa muhallansu daga tashe tashen hankula a arewa maso gabas, damarsu ta tsira ta kasance ne wajen zabar ko su zauna a gidajensu ko kuma su fice. Yayin da tserewar Mary Oyuba tayi nasara, wasu da yawa ba su yi sa'a ba. Marubuciya: Zubaida Baba IbrahimMuryoyin Shiri: Khadija GidadoFassara: Rukayya Saeed   Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija GidadoBabban Furodusa: Anthony AsemotaBabban Mashiryi: HumAngle Media
loading
Comments 
Download from Google Play
Download from App Store