Mu Zagaya Duniya

<p>Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.</p>

Dawowar sace-sacen ɗalibai daga makarantunsu a Najeriya

Shirin zai fara ne da batun tsaro a tarayyar Najeriyar, lamarin da ya fi ɗaukar hankali a ciki da wajen ƙasar sakamakon ƙaruwar da matsalolin rashin tsaron suka yi a cikin ‘yan kwanaki, lamarin da ya kai ga dawowar sace-sacen ɗalibai daga makarantunsu baya ga wasu hare-haren da ‘yan bindigar ke kai wa suna salwantar da rayuka a sassan Najeriyar musamman ma a yankin arewacin ƙasar.

11-29
20:07

Sabbin hare-haren da 'yan bindiga suka ƙaddamar a jihohin Najeriya

A wannan mako shirin Mu Zagaya Duniya ya faro ne daga hare-haren da 'yan bindiga suka ƙaddamar a Najeriya, inda suka sace ɗalibai 25 a makarantar sakandiren Maga ta jihar Kebbi, da kuma harin da suka kai mujami'ar jihar Kwara, sai na Zamfara, da Sokoto, da Borno da kuma Neja. Shirin ya kuma leƙa sauran ƙasashen Afrika da ma Nahiyar Turai, don yin bitar labaran da muka kawo muku a makon da muke bankwana da shi. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...

11-22
20:08

Dambarwar siyasar da ta dabaibaye jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya

Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman a wannan mako kamar yadda ya saba ya yi bitar muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi daga ɓangarori daban-daban na duniya. A Najeriya shirin ya faro da batun Siyasa inda a cikin makon da muka yi wa bankwana rikicin cikin gidan babbar Jam’iyyar adawar Najeriyar wato PDP ya zama ɗaya daga cikin batutuwan da suka ɗauki hankali. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

11-15
19:39

Trump ya nanata barazanar ɗaukar matakin soji kan sansanonin ‘yan ta’adda a Najeriya

A ranar Larabar da ta gabata shugaban Amurka Donald Trump ya nanata barazanar ɗaukar matakin soji na ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin ‘yan ta’adda a Najeriya, inda kuma ya ƙara caccakar gwamnatin ƙasar kan gaza ɗaukar matakin hana kisan kiyashin da ya ce ana yi wa Kiristoci a ƙasar.

11-08
20:09

Bitar muhimmn labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi

A cikin wannan shiri tare da Nura Ado Suleiman, kamar kowanne mako ya kan yi bita ne kan wasu daga cikin muhimman labaran da suka faru a makon da muke shirin yin bankwana da shi. Cikin waɗannan labarai kuwa akwai yadda aka sanar da sakamakon zaɓen Kamaru wanda ya kai ga ɓarkewar zanga-zangar adawa da wannan sakamako da ke nuna shugaba Paul Biya mai shekaru 92 a matsayin wanda ya yi nasara da fiye da kashi 53 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa. Ku latsa alamar sauti don auraron cikakken shirin.

11-01
20:09

Shuban Tinubu na Najeriya ya sallami manyan hafsoshin tsaron ƙasar

Daga cikin labarun da shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan makon ya kunsa akwai labarin matakin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ɗauka na yin tankaɗe da rairaya a manyan hukumomin tsaron ƙasar, inda ya sallami manyan hafsoshin tsaron ƙasar, dai dai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe ‘yan ta’adda fiye da 50 yayin wasu jerin hare-hare da mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar kusan lokaci guda a kan garuruwan daban daban a jihohin Borno da Yobe. Shirin ya waiwayi wasu daga cikin lamurran da suka wakana a Kamaru inda ake cigaba da dakoon Kotun Fasalta Kundin tsarin mulki ta tabbatar da sakamakon zaɓen shugabancin ƙasar. A yankin gabas ta tsakiya, Amurka ta hau kujerar naki kan yunƙurin wasu na ganin Isra’ila ta kwace iko ya yankin Falasɗinu na Gaɓar yamma da kogin Jordan.

10-25
18:30

Trump ya jagoranci ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Daga cikin labarun da shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan makon akwai yarjejeniyar zaman lafiyar da shugabannin ƙasashen yankin Gabas ta tsakiya suka ƙulla a ƙarƙashin jagrancin takwaransu na Amurka Donald Trump, sai kuma waiwayar halin da ayyukan agaji ke ciki a Zirin Gaza, bayan tsagaita wutar da aka yi tsakanin Isra’ila da Hamas. A Najeriya kuwa shirin zai waiwayi taron da Malamn Addinin Musulunci suka yi a Kaduna  kan yadda amfani da kafafen sadarwa na zamani ba bisa ka’ida ba gami da tattaunawa kan lamurran da suka shafi tsaro da tabarbarewar tattalin arziki. Sai kuma ziyarar da Ministan harkokin wajen Faransa Jean Noel Barrot ya kai ƙasar. Muna kuma ɗauke da rahotanni kan lamurran da suka wakana a Kamaru cikin makon da muka yi wa adabo, inda ake ci gaba da dakon fitar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Nura Ado Suleiman.............

10-18
19:59

Dubban Falasɗinawa sun fara tururuwar komawa muhallansu a yankin arewacin Gaza

Daga cikin labarun da shirin 'Mu zagaya Duniya' tare da Nura Ado Sulaiman, ya waiwaya a wannan makon akwai halin da ake ciki a Zirin Gaza bayan yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin da aka samu nasarar ƙullawa tsakanin Isra’ila da Hamas.Shirin ya kuma waiwayi zaɓen shugabancin Kamaru wanda masu fashin baƙi ke ci gaba da tofa albarkacin bankinsu a kai. A najeriya kuma akwai waiwayen afuwar da shugaba Bola Tahmed Tinubu ya yi wa wasu mutane fiye da 170 Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...........

10-11
20:02

Najeriya ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da samun 'yancin kai

Daga cikin batutuwan da shirin ya waiwaya a wannan mako akwai,taƙaddamar da ke tsakanin ƙungiyar PENGASSAN da matatar mai Ɗangote a Najeriya, sai kuma bikin cika shekaru 65 da Najeriyar ta yi. Zaku ji yadda ake ƙara samun ɓarkewar zanga-zanga a wasu Ƙasashen Afrika.

10-04
20:38

Faransa ta jagoranci gwamman ƙasashen Turai wajen amincewa da ƙasar Falasɗinu

A cikin wannan shirin da ke waiwaye kan mahimman labaran wannan makon, za ku ji cewa:  Faransa ta jagoranci ƙarin gwamman ƙasashe wajen amincewa da Yankin Falasɗinu a mamtsayin ƙasa ‘Yantacciya a wani yunƙuri na Diflomasiya da ke zama ɗaya daga cikin mafiya girma da aka gani cikin shekaru da dama.   Shirin zai kuma waiwayi jawaban wasu daga cikin shugabannin Nahiyar Afrika a zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya. Najeriya ta yi fatali da rahoton Amurka da ya zargi mahukuntan ƙasar da gazawa sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na aiwatar da ayyukan raya ƙasa da akw warewa maƙudan kuɗaɗe a kasafi duk shekara. Da dai sauran mahimman labarai.

09-27
20:01

Dillalan mai a Najeriya sun nemi tallafin naira tiriliyan 1 daga matatar Ɗangote

Dillalan man fetur da masu rumbunan ajiyar mai a Najeriya sun buƙaci a riƙa biyan su tallafin sama da naira tiriliyan 1 duk shekara domin kawar da asarar da suka ce su na tafkawa, a Larabar makon jiya ne Ministocin shari’ar  ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar sun kammala taronsu da suka tattauna kan batutuwan da suka shafi  shari'a da kare Haƙƙin bil'adama, wasu kenan daga cikin manyan labarun makon jiya da Nura Ado Suleiman zai kawo muku a cikin shirin Mu zagaya Duniya.. Latsa alamar sauti don sauraron shirin..........

09-20
19:39

Shirin ƙarin albashin masu riƙe da muƙaman siyasa a Najeriya ya bar baya da ƙura

A karon farko gwamnatin Najeriya ta hannun hukumarta da ke kula da sufurin jiragen ruwa a koguna ko kuma cikin gida, ta shelanta haramta jigilar duk wani jirgi ko kwale-kwale da ba a yi wa rijista da gwamnati ba, Ghana ta karɓi baƙi ‘yan Afirka ta yamma, waɗanda gwamnatin Amurka ta taso ƙeyarsu a ƙarƙashin shirin shugaba Donald Trump na korar baƙin-haure, wasu kenan daga cikin manyan labarun makon jiya da Nura Ado Suleiman zai kawo muku a cikin shirin Mu zagaya Duniya.. Latsa alamar sauti don sauraron shirin..........

09-13
20:00

Najeriya ta sha alwashin shigar da ƴan ƙasar aƙalla miliyan 44 cikin tsarin inshorar lafiya

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin shigar da ƴan ƙasar aƙalla miliyan 44 cikin tsarin inshorar lafiya nan da shekara ta 2030,Iftila’in zabtarewar ƙasa ya lakume rayukan mutane fiye da dubu 1 a Sudan,wasu kenan daga cikin manyan labarun makon jiya da Nura Ado Suleiman zai kawo muku a cikin shirin Mu zagaya Duniya.

09-06
19:54

ECOWAS na shirin kafa rundunar soji mai dakaru sama da dubu 250

Daga cikin batutuwan da shirin ya waiwaya akwai taron da Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Afrika suka yi kan  matsaloli musamman na ta’addanci  da suka addabi nahiyar. Sai shirin ƙungiyar ƙasashen ECOWAS na haɗa makekiyar rundunar haɗin gwiwa irinta ta farko, da za ta ƙunshi  dakaru dubu 260,000 Akwai bitar rahoton binciken da ya gano ƙaruwar yawan attajirai a Nahiyar Afrika Sai kuma zaman da kwamitin tsaron Majlisar Ɗinkin Duniya ya yi kan halin da ake ciki a Zirin Gaza, yankin da a Juma’ar nan da ta gabata Isra’ila ta dakatar da shigar da kayan abinci zuwa cikin babban birninsa.

08-30
19:57

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi shelar ɓarkewar bala’in Yunwa a zirin Gaza

Karon farko Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi shelar ɓarkewar bala’in Yunwa a zirin Gaza, tashin hankalin da a hukumance ba a taɓa ganin makamancinsa ba a Yankin Gabas ta Tsakiya.Muhawara ta dawo sabuwa a Najeriya a tsakanin masu ganin dacewar yin Sulhu da ‘yan bindiga da kuma masu ra’ayin kawai a ci gaba da yi ɓarin wuta domin ko da an sulhunta, komawa ta’addancinsu suke yi a duk sanda suka so. 

08-23
20:01

Bitar mako: Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar kashe ‘yan ta’adda kusan 600

Wasu daga cikin labarun makon da ya gabata da shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya waiwaya a wannan karon sun haɗa da, nasarar da rundunar Sojin Najeriya ta samu na kashe ‘yan ta’adda kusan 600 da yarjejeniyar sayen makamai da ƙasar ta ƙulla da Amurka. Sai kuma a fannin tattalin arziƙi, inda wata tawaga ta musamman daga ƙasar Qatar ta fara ziyarar makwanni kusan 3 a wasu ƙasashen nahiyar Afrika domin ƙulla yarjeniyoyi gami da zuba hannayen jarin biliyoyin Dalar Amurka a ƙasashen aƙalla 10.

08-16
19:59

Bitar labaran mako: Hatsarin jirgi mai sauƙar ungulu ya girgiza al'ummar Ghana

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman kamar kullum ya yi bitar wasu daga cikin labarai da suka fi daukar hankali a makon da muka yi bankwana da ita, masamman yadda Isra’ila ke shan caccaka daga ƙasashe da dama biyo bayan alwashin da ta sha na mamaye ilahirin yankin Zirin Gaza, Sai kuma Ghana inda aka shafe kwanaki ana makoki sakamakon rasa rayukan wasu daga cikin ministocinta a haɗarin jirgi mai saukar ungulu da ya rutsa da su. 

08-09
19:17

Gwamnatin Katsina ta tabbatar da kashe jami’an tsaro 130 da ƴan ta'adda suka yi

A cikin shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon tare da Rukayya Abba Kabara ya waiwayi yadda gwamnatin jihar Katsina ta Najeriya, ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Radda ta tabbatar da mutuwar jami’an tsrao 130 a hannun yan ta’adda. Shirin ya kuma waiwayi  yadda ƙasashen duniya ciki har da Faransa suka nuna gamsuwarsu da samar da ƴantacciyar ƙasar Falaɗinu, don tabbatuwar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.............

08-02
21:16

Tsaffin jami’an ƴansanda a Najeriya sun gudanar da kwarya-kwarayar zanga-zanga

Masu saurare barkan mu da safiya Rukayya Abba Kabara ce ke farincikin kasancewa da ku a cikin sabon shirin Mu zagaya Duniya,a cikin shirin zaku ji yadda mutane sama da miliyan biyar ke fama da tsananin yunwa a wasu jihohin arewa maso gabashin Najeriya uku. Wannan mako ne tsaffin jami’an ƴansanda a Najeriya suka gudanar da wata kwarya-kwarayar zanga-zanga a babban birnin tarayyar Abuja.

07-26
20:00

Yan Najeriya na alhinin rasuwar tsofan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Shirin Mu zagaya Duniya na wanan makon tare da Ibrahim Mallam Tchilla yayi waiwaye kan  gudunmawar da tsofan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayer wajen hada kai da samar da cigaba ga al'umma Najeriya. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin....

07-19
20:15

Recommend Channels