Najeriya za ta bayar da damar shigar da kayan abinci ba tare da haraji ba
Description
Shirin duniya kamar yadda aka saba na duba manyan labaran da suka faru a sassan duniya
A cikin shirin zaku ji cewa..............
Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin janye biyan kudaden haraji kan wasu muhimman kayayyakin abinci da ta dage haramcin shigar da su kasar, don saƙaƙawa jama’a raɗaɗin tsadar raywar da suke ciki.
Matakin sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar, Mali da kuma Burkina Faso na tabbatar da ballaewarsu daga ECOWAS ya tayar da hankalin kungiyar kasashen ta yammacin Afirka, a yayin da kwararru ke cigaba da bajakolin ra’ayoyinsu kan matakin.
A Kenya kuwa, shugaban ƙasar William Ruto ne ya kori rankatakaf din ministocinsa sai fa ƙwaya biyu rak da ya bari, ‘yan kwanaki bayan zanga-zanga kan tsadar rayuwa da dubban matsasan kasar suka gudanar.
Danna alamar saurare don jin gundarin shirin tare da Nura Ado Sulaiman.