Zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa ta rikiɗe zuwa tarzoma a sassan Najeriya
Update: 2024-08-03
Description
Mu Zagaya Duniya, shiri ne da ya saba tacewa gami da zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare domin bitarsu tare da Nura Ado Suleiman.
Shirin wannan makon ya fi mayar da hankali ne wajen bitar yadda zanga-zanga kan tsadar rayuwa da kuma neman shugabanci nagari ta gudana a sassan Najeriya, inda a wasu sassa zanga-zangar ta lumana ta rikiɗe zuwa tashin hankalin da ya kai ga hasarar rayuka da kuma ɗimbin dukiya.
'Mu Zagaya Duniya' zai kuma leka Mali, inda dakarun kasar da dama gami da sojojin hayar Rasha na Kamfanin Wagner suka rasa rayukansu, bayan ƙazamin artabun da suka yi da mayakan Abzinawan da suka samu taimakon masu tayar da kayar bayan dake ikirarin jihadi.
Comments
Top Podcasts
The Best New Comedy Podcast Right Now – June 2024The Best News Podcast Right Now – June 2024The Best New Business Podcast Right Now – June 2024The Best New Sports Podcast Right Now – June 2024The Best New True Crime Podcast Right Now – June 2024The Best New Joe Rogan Experience Podcast Right Now – June 20The Best New Dan Bongino Show Podcast Right Now – June 20The Best New Mark Levin Podcast – June 2024
In Channel