DiscoverMu Zagaya Duniya
Mu Zagaya Duniya
Claim Ownership

Mu Zagaya Duniya

Author: RFI Hausa

Subscribed: 24Played: 208
Share

Description

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

217 Episodes
Reverse
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Nura Ado Sulaiman kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata, ciki kuwa har da batun yaddama’aikatar tsaron Najeriya ta bakin hafsan hafsoshin sojin ƙasar Janar Christopher Musa ta sanar da cewa cikin watanni 6 na ƙarshen wannan shekara adadin ƴan ta’adda dubu 129 da 417 tare da iyalansu ne suka ajje makamai bayan miƙa wuya ga mahukuntan ƙasar, lamarin da ke matsayin gagarumar nasara a ƙoƙarin da Najeriya ke yi na kawo ƙarshen barazanar ta’addancin da ya yi mata katutu. 
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Nura Ado Sulaiman kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata, ciki kuwa har da batun yadda  Hukumar Kula da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta sanya hawan Dabar jihar Kano dake Najeriya cikin manyan Al’adun Duniya masu dimbin Tarihi.Da kuma sauran rahotanni da suka gabata.Sai a latsa alamar sauti domin samun cikakken shirin.
Masu sauraro Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin sabon shirin Mu Zagaya Duniya, wanda ke waiwayar wasu daga cikin muhimman lamuran da suka faru a makon da ya ƙare.......Akwai tsokaci ko kuma martani daga ɓangarori daban daban  dangane da umarnin kotun duniya ta ICC na bada sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa da kuma ɗaya daga cikin Jagororin  Mayakan Hamas.
Mu zagaya  Duniya

Mu zagaya Duniya

2024-11-0921:41

Shirin mu zagaya Duniyaya yi dubi da yadda zaben Amurka ya gudana. Karibullah Abdulhamid na Madobi ya gabatar.
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Ƙaribullah Abdulhamid Namadobi kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke shirin bankwana da shi, ciki kuwa har da batun matsalar wutar lantarkin da yankin Arewacin Najeriya ya yi fama da shi, sai kuma shirye-shiryen tunƙarar zaɓen Amurka da ke tafe a makon gobe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin wanda ya taɓo ɓangarori daban-daban na duniya kama daga Afrika da nahiyar Turai, Asiya da kuma tashe-tashen hankulan da ake fama da su a sassan duniyar musamman gabas ta tsakiya.
Daga cikin labarun da shirin ya waiwaya akwai, korafin da kungiyar direbobin motocin haya a Najeriya ta gabatar da korafi kan tashin hankalin da mabobinta ke fuskanta, inda ta gabatar da kididdigar da ke nuna cewar, akalla direbobi 50 ‘yan ta’adda suka halaka suka kuma suka yi awon gaba da wasu mutanen da dama daga kan hanyar Gusau zuwa Funtua.Al’ummar Jamhuriyar Nijar na alhinin rashin da suka yi na tsohon Fira Ministan kasar Hama Amadou, wanda ya rasu a ranar Larabar da ta gabata.
Yayin da ‘Yan Najeriya da dama ke jin jiki kan matsin rayuwar da suka shiga tun bayan janye tallafin man fetur da kuma fara aiwatar da wasu matakai da sabuwar gwamnatin ƙasar  ta yi, Bankin Duniya yayi gargaɗin cewar, matsalar da ake ciki samin taɓi ce, muddin aka kuskura aka janye ko dakatar da manufofin tattalin arziƙin da shugaba Tinubu ke aiwatarwa.
Shirin Mu Zagaya duniya tare da Nura Ado Suleiman kamar ko yaushe ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi, ciki kuwa har da ƙarin farashin man fetur ta Najeriya ta sake yi karo na 4 cikin watanni 16 duk da matsi da tsadar rayuwa da ta addabi al'ummar ƙasar.
Daga cikin  Labarun da suka fi ɗaukar hankali a makon da ya ƙare akwai jerin makamai masu linzamin da Iran ta kai wa Isra’ila hari da su, a yayin da ita kuma Isra’ilar ta karkatar da hare-haren da take kai wa a Gaza zuwa Kudancin Lebanon, h da zummar murkushe mayakan Hezbolla A Najeriya kuwa ɗimbin Iyallai ne suka shiga alhinin rashin da suka yi, biyo bayan nuutsewar da wani jirgin ruwa yayi ɗauki da fasinjoji sama da 300 da ke ƙoƙarin tsallaka kogin Kwara domin zuwa taron Maulidi.
Daga cikin labarun da shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya waiwaya, akwai yadda babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya gudana, haka nan akwai bitar rahoton maƙudan ƙuɗaɗen da ECOWAS ta ware don samar da wutar lantarki a makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya, a wasu ƙasashen da ke ƙarƙashinta ciki har da Najeriya, haka nan shirin ya waiwari halin da ake ciki game da rikicin Isra'ila da Hezbollah a Lebanon. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.......
Har yanzu tsuguni bata kare ba tsakanin kamfanin Dangote da kamfanin NNPC dangane da gabatar da man fetur da yake tacewa a cikin gida. A cikin wannan shirin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Kasum Kurfi, masanin tattalin arziki da kuma Abdulkarim Ibrahim dangane da kalubale da kuma mafita dangane da wannan al'amari.
Daga cikin labarun da shirin makon nan ya waiwaya akwai iftila’in ambaliyar ruwan da ya afka wa garin Maiduguri babban birnin jihar Borno da kuma halin da aka shiga bayan aukuwar lamarin.A fannin tsaro kuwa, dakarun sojin Najeriya ne suka samu nasarar halaka ɗaya daga cikin manyan jagororin ‘yan ta’addan da suka addabi al’ummar yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Matsalar tsaro na ci gaba da ta'azzara a yankin arewa maso yammacin Najeriya, musamman a yan makwannin da suka gabata, inda 'yan bindiga ke kai hare hare suna kashewa ba tare da kaukauatawa ba. Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tace tana iya bakin kokarin ta amma kuma jama'a na cewar har yanzu da sauran aiki.
Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Rukayya Abba Kabara ya taɓo halin da aka shiga a Najeriya bayan da mahukunta suka kara farashin man fetur, sai kuma taron Afirka da China da kuma sabon fraministan Faransa.
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya taɓo batun sake dawo da alaka da aka yi tsakanin Najeriya da Nijar, da yadda aka samu karuwan basukan da kasashen Afrika ke ciwowa daga China da kuma batun neman sanyawa wasu ministocin Isra'ila takunkumi da ƙungiyar tarayyar Turai ta nema mambobinta su yi.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh....
Shirin Mu zagaya Duniya da ke bitar labaran mako tare da Nura Ado Suleiman ya taɓo yadda ambaliyar ruwa ke ci gaba da ɓarna a sassan arewacin Najeriya a wani yanayi da hukumar NEMA ke gargaɗi kan yiwuwar ambaliyar ta shafi mutane fiye da miliyan 3 a jihar Kano kaɗai.
Shirin mu zagaya duniya na wannan mako ya duba manyan labaran da suka faru a wannan mako ciki kuwa har da addin mutanen da hare-haren ta'addanci suna kashe a cikin shekaru biyar a Najeriya Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman
Mu Zagaya Duniya, shiri ne da ya saba tacewa gami da zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare domin bitarsu tare da Nura Ado Suleiman. Shirin wannan makon ya fi mayar da hankali ne wajen bitar yadda zanga-zanga kan tsadar rayuwa da kuma neman shugabanci nagari ta gudana a sassan Najeriya, inda a wasu sassa zanga-zangar ta lumana ta rikiɗe zuwa tashin hankalin da ya kai ga hasarar rayuka da kuma ɗimbin dukiya.'Mu Zagaya Duniya' zai kuma leka Mali, inda dakarun kasar da dama gami da sojojin hayar Rasha na Kamfanin Wagner suka rasa rayukansu, bayan ƙazamin artabun da suka yi da mayakan Abzinawan da suka samu taimakon masu tayar da kayar bayan dake ikirarin jihadi.
A ranar Alhamis da ta gabata, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naira dubu 70 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, inda yayi alƙawarin sake nazari kan yiwuwar wani ƙarin a duk bayan shekaru uku, a cikin shirin mu Zagaya Duniya ,Nura Ado Suleiman ya  zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare domin bitarsu.
Shirin duniya kamar yadda aka saba na duba manyan labaran da suka faru a sassan duniya A cikin shirin zaku ji cewa..............Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin janye biyan kudaden haraji kan wasu muhimman kayayyakin abinci da ta dage haramcin shigar da su kasar, don saƙaƙawa jama’a raɗaɗin tsadar raywar da suke ciki.Matakin sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar, Mali da kuma Burkina Faso na tabbatar da ballaewarsu daga ECOWAS ya tayar da  hankalin kungiyar kasashen ta yammacin Afirka, a yayin da kwararru ke cigaba da bajakolin ra’ayoyinsu kan matakin.A Kenya kuwa, shugaban ƙasar William Ruto ne ya kori rankatakaf din ministocinsa sai fa ƙwaya biyu rak da ya bari, ‘yan kwanaki bayan zanga-zanga kan tsadar rayuwa da dubban matsasan kasar suka gudanar.Danna alamar saurare don jin gundarin shirin tare da Nura Ado Sulaiman.
loading