Ilimi Hasken Rayuwa

<p>Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’Adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.</p>

Rashin albashi na shafar aikin koyarwa a makarantu masu zaman kansu a Najeriya - Rahoto

A wannan makon, shirin yayi dubi ne kan batun yadda har kawo yanzu ake samun malaman makaratu masu zaman kansu a Najeriya dake ɗaukar albashin Naira dubu 15 zuwa sama, maimakon mafi ƙaranci albashin naira dubu 70 da gwamnati ƙasar ta yi dokar biya. Duk da irin kuɗaden da ake shatawa iyayen yara, har ta kai idan yaronka ba a biya mishi kuɗin makaranta ba, to kuwa za a kora maka shi gida, hakan be sanya sun inganta albashin malaman ba. Makaranta mai zaman kanta mutum ke kafa ta ko haɗin gwiwa na wasu mutane domin taimakawa ko ba gudunmawa yayin da a wannan lokaci da dama sun mayar da ita matsayin kasuwanci, abin da masana ke ganin kenan akwai buƙatar Malamai su samu yanayi mai kyau da walwala wanda ta hakanne zasu samu ƙwarin gwiwa wajan bayar da ilimi mai nagarta. Hauwa'u Adam dake koyarwa a wata Makarata dake yankin Jambulo a jihar Kanon Najeriya, ta sheda mana cewa saboda karatunta yakai matakin digiri ne ake biyanta Naira dubu 20, amma masu kwalin babbar difloma ta HND da NCE albashin daga dubu 17 ne zuwa 18 Masana da masu fashin baki na ganin cewa, gwamnatoci sun yi sakaci sosai, musamman ta hanyar sakarwa makarantu masu zaman kansu linzami suna abin da suka ga dama, idan kaji mahukunta na kai ruwa rana da su to kuwa baya wuce akan haraji ne.

12-02
10:06

Makomar ilimi dalilin rufe makarantu sabida matsalar tsaro a Najeriya

A wannan makon shirin ya karkata akala ne kan makomar ilimi a Najeriya, inda hukumomi suka fara rufe makarantu saboda matsalolin tsaro da ke neman dakushe makomar ilimin manyan gobe. Me yasa jihohi ke gaggawar rufe makarantu bayan sace ɗalibai a Kebbi da Niger a kwanan nan? Shin babu wasu hanyoyin kawo ƙarshen matsalar tsaro sai dai rufe makarantu?   Tambayar kenan da ‘yan Najeriya ke yiwa gwamnatin ƙasar, yayin da ake ganin tarin jami’an tsaro na yiwa masu rike da manyan makamai rakiya, abin da ke nuna yawan jami’an tsaron da ƙasar ke da shi idan aka haɗa ƴansanda da sojoji da jami’an tsaron Civil Defence da sauransu, to kuwa iyaye suka ce idan har aka yi la’akari da wannan za a iya samarwa ɗalibai tsaro. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.........

11-25
10:00

Har yanzu Malama tsangaya na amfani da Ajami wajen musayar sakonni

Shirin a wannan mako, kareshe ne kan maudu’in da muka tattaunawa a makonni biyun da suka gabata, wanda ya mayar da hankali kan yadda rubutun Ajami a kasar Hausa ya yi shura, da kuma yadda yake neman bacewa a wannan zamani. Yayin da ake ganin har yanzu a Jamhuriyar Nijar, akwai yankunan da suke amfani da ajami wajen isar da sakonni, Malaman tsangaya daga Najeriya ma suna amfani da wannan tsarin rubutu wajen musayar bayanai a tsakaninsu. Yaɗuwar addinin Islama a Ƙasar Hausa masana suka ce, ya taimaka sosai wajen shaharar wannan salo na rubutu, sannan kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen inganta hanyoyin sadarwa na wancan lokaci. A tattaunawarmu da masanin tarihi daga Kanon Najeriya, farfesa Tijjani Naniya, ya bayyana cewa, zuwan turawan mulkin mallaka, shine musabbabin gushewar wannan rubutu a kasar Hausa, amma a wancan lokaci, rubutun na ajami ya ci kasuwa tsakanin masana, malamai, sarakuna da kuma ‘yan kasuwa.

11-11
09:59

Tasirin rubutun Ajami wajen musayar bayanai tsakanin al'ummar Hausawa ( 2)

Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya cigaba ne da mayar da hankali kan makomar rubutun Ajami a ƙasar Hausa, nau'in rubutun da ya taimaka matuƙa wajen musayar bayanai tsakanin al'ummar Hausawa tun gabanin zuwan Turawan mulkin mallaka.     A shekarun baya-bayan nan rubutun na Ajami ya zama tarihi a ƙasar Hausa bayan da kowanne ɓangare ya rungumi tsarin boko daga turawan Yamma. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin kashi na biyu:

11-04
10:10

Tasirin rubutun Ajami wajen musayar bayanai tsakanin al'ummar Hausawa

Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan makomar rubutun Ajami a ƙasar Hausa, nau'in rubutun da ya taimaka matuƙa wajen musayar bayanai tsakanin al'ummar Hausawa tun gabanin zuwan Turawan mulkin mallaka. A shekarun baya-bayan nan rubutun na Ajami ya zama tarihi a ƙasar Hausa bayan da kowanne ɓangare ya rungumi tsarin boko daga turawan Yamma. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

10-28
09:26

Yadda dokar rage kuɗin makaranta za ta yi tasiri ga tsarin Ilimi a Nijar

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan dokar da ta tilastawa makarantu masu zaman kansu rage kudin makaranta da gwamnatin Nijar ta kafa, wanda ke zuwa bayan ƙarin hutun makarantu na makwanni biyu saboda mamakon ruwan a ƙasar ta yankin Sahel. Ƙarƙashin wata doka da shugaban gwamnatin Sojin Nijar Abdourraham Tchiani ya sanya hannu ce ta buƙaci dukkanin makarantun su rage kuɗin da suke karɓa da kashi 20, kodayake wannan doka bata shafi makarantun da ke karɓar kuɗin da bai kai CFA jaka hamsin ba. Tuni iyaye suka yi maraba da wannan mataki. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

10-14
10:00

Malamai a Najeriya na fuskantar tarin matsaloli saboda rashin kyawun albashi

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali kan gudunmawar malaman makaranta ga rayuwar jama'a dai dai lokacin da aka gudanar da bikin ranar Malamai a sassa daban-daban na duniya. Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware wannan rana da nufin girmama gudunmawar da malaman ke bayarwa, sai dai an gudanar da wannan rana ne a dai dai lokacin da malamai a Najeriya dama sauran ƙsashen Afrika ke ganin ƙololuwar matsin rayuw sakamakon matsalolin da suka dabaibaye su kama daga rashin kyawun yanayin aiki dama ƙarancin albashi. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...

10-07
10:00

Yadda aikin gona ke hana dimɓin yara zuwa makaranta a Najeriya

Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya duba yadda wasu manoma a Najeriya, musamman arewacin kasar ke hana yaransu zuwa makaranta, har sai an yi girbin amfanin gona, saboda wasu dalilai Ku shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

09-30
09:34

Yadda bikin kammala karatu ke taka rawa wajen lalata tarbiyyar Ɗalibai

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda bikin yaye ɗalibai da ɗabi'ar rubutu a jikin rigunan juna dama sauran shagulgulan da akanyi a bikin na kammala makaranta ke taka muhimmiyar rawa wajen lalata tarbiyyar ɗalibai. Tsawon shekaru aka ɗauka wannan dabi'a na ciwa iyaye tuwo a ƙwarya dama sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren tarbiyyar al'umma. Sai dai bayan tsanantar ƙorafe-ƙorafe kan wannan ta'ada, kwatsam an wayi gari gwamnatin jihar Kaduna ta yi uwa da makarɓiya wajen haramta irin bukukuwan har ma da wasu ƙarin dokoki da suka shafi sashen na ilimi ciki har da haramtawa makarantu ƙarin kuɗin makaranta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

09-23
09:40

Yadda ake fama da ƙarancin malamai a makarantun jihar Jigawa ta Najeriya

Shirin na wannan rana zai ɗora kan wanda muka gabatar muku a makon jiya game da karancin malamai a makarantun jihar Jigawa ta arewacin Najeriya. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

09-16
09:54

Yadda Nijar ta bijiro da sabon tsarin karatu na bada ƙarin horo lokacin hutu

Shirin ilimi Hasken rayuwa na wannan rana ya mayar da hankali ne kan tsarin koyarwa da Nijar ke yi na baiwa dalibai karin horaswa akan darussa masu wahala a lokutan hutu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

09-09
09:36

Matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da kafa makarnatun gaba da sakandare

Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako ya duba matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da kafa makarantun gaba da sakandare a fadin ƙasar har na tsawon shekaru 7, mataakin da ya biyo bayan wani zama da majalisar zartaswar ƙasar ta yi a ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu. Majalisar ta ce babu amfanin kafa makarantun da ba za a samu abin da ake buƙata ba, a maimakon haka zai kyautu a inganta waɗanda ake da su.

09-02
10:22

Makarantun Firamare sun fara koyarwa da harshen Hausa don sauƙaƙa koyo a Kano

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda wasu daga cikin Makarantun Firamare a jihar Kano suka koma koyarwa da harshen Hausa da nufin sauƙaƙa koyo da koyarwa tsakanin yaran jihar. Kafin yanzu dai akwai dokar da ta soke koyarwa da harsunan gida 3 a Makarantun Najeriyar da suka ƙunshi Hausa da Yarabanci da kuma Igbo, inda tuni aka ga yadda wasu Makarantu suka daina koyarwa da wannan harshe, kodayake tun tuni dama yankin kudancin Najeriya ya yi watsi da wannan doka tare da ci gaba da koyar da harsukan. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

08-26
09:26

Tsarin cigaban manyan malaman jami'a a Jamhuriyar Nijar

Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai duba tsarin cigaban manyan malaman jami'a a Jamhuriyar Nijar, wanda ke kai su ƙololuwa a harkar ilimi. Domin samun ingataccen ilimi, dole ne a samu ƙwararrun malamai da za su koyar da ɗalibai da ke karatu a fannoni dabam-dabam. haka zalika malaman da ke koyarwar su ma su na neman hanyoyin ƙara ƙwarewa don kai wa ƙololuwa a aikin na su na koyarwa.

08-19
09:55

Ƙalubalen da shirin amfani da harshen Uwa a makarantun Najeriya ke fuskanta

Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' a wannan makon ya mayar hankali ne akan makomar amfani da harshen uwa a makarantun Najeriya, inda ya yi dubi da cigaba da kuma akasi. Masana dai sun tofa albarkacin bakinsu akai. Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta shelantar fara amfani da  harshen uwa wajen bayar da ilimi musamman a matakin farko, masana da masharhanta suka fara sharhi kan ƙalubalen da shirin zai iya fuskanta idan aka fara aiwatar da shi.

08-12
09:48

Najeriya: Dakatar da ciyarwa a makarantu ya durƙusar da karatun wasu ɗalibai

A Najeriya dakatar da tallafin ciyarwa da gwamantocin ƙasar suka yi a Makarantun wasu sassan ƙasar musamman arewaci ta haifar da ƙafar Ungulu ga himmar zuwa makarantu a tsakanin ɗalibai da Iyayensu. Wasu Iyaye da aka zanta dasu sun ce shirin tallafin na taka muhimmiyar rawa wajen sama musu sassauci wajen ciyar da 'ya'yan nasu, amma daga bisani aka ci karo da tsaiko. Sai a latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiya Haruna.

07-29
09:56

Tasirin makarantar koyar da harshen Larabci ta SAS ga Arewacin Najeriya 2

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan tasirin da Makarantar koyar da harshen Larabci ta ASA a Kano ta yi wajen yaye fitattun mutane a matakai daban-daban musamman a ɓangaren shari'a kodayake Makaranta na fuskantar koma baya a yanzu. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

07-22
10:03

Ghana ta fara wani yunƙuri inganta tsarin koyo da koyarwa da binciken Likitanci

Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako, shirin da bisa al'ada ke taɓo batutuwan da suka shafi ilimin kimiyya da fasaha ko ƙere ƙere, baya lalubo ƙalubale ko kuma ci gaban da waɗannan fannoni suka samu. A wannan makon, shirin ya yada zango a Ghana inda zakuji yadda mahukuntan Ghana suka bullo da wani matakin inganta ilimin likitoci bayan miƙa cibiyar kimiyya da Fasaha ga babbar Jami'ar ƙasar, wanda zai taimaka wajen binciken kimiyya da fasaha. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

07-16
09:57

Tasirin makarantar koyar da harshen Larabci ta SAS ga Arewacin Najeriya

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan tasirin da Makarantar koyar da harshen Larabci ta ASA a Kano ta yi wajen yaye fitattun mutane a matakai daban-daban musamman a ɓangaren shari'a kodayake Makaranta na fuskantar koma baya a yanzu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

07-08
10:11

China na shirin fara tarfo hasken Rana kai tsaye daga wajen Duniya

Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan rana ya mayar da hankali ne kan shirin China na samar da wata tasha ta samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, wadda zata riƙa zuƙo hasken rana kai tsaye daga sararin samaniya ba tare da samun tarnaƙi daga giza-gizai ba.

07-01
09:32

Recommend Channels