HausaRadio.net

HausaRadio.net - Online Hausa Radio

"Daga Laraba" 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao

Daga Laraba 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao Ga shirin mu na podcast wanda Halima Djimrao ce ta jagoranta tare da sauran abokan aiki. Shiri ne akan yadda ƴan ƙabilar Igbo Musulmi ke cikin tsangwama da barazana a yankin su na kudu maso gabashin Najeriya, saboda haka da yawan su, sun gwammace su yi hijira zuwa arewa. Podcast Trailer: https://youtu.be/qzLb2V9521U

05-24
16:11

Komai muka samu mu fassara zuwa yaren mu Hausa - Malam Habibu Sani Babura

Allah akbar! Wannan muryar marigayi, Malam Habibu Sani Babura kenan, yayin da yake lacca a wajen taron daliban Hausa  a Jami'ar Bayero ta Kano. Yau shekara biyu da rasuwar Malam (3/8/2018. Allah ya jikansa da rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya Sada shi da Annabi, Allah ya bashi aljanna Firdausi).

09-04
03:28

#RanarHausa 2020-08-25 Arewa Radio 93.1's Program with BANNigeria

Shirin Arewa Radio kan #RanarHausa2020 tare da Faisal Abdullahi (@BANNigeria) da Mazhun (@HausaTranslator) na Bloggers Association of Northern Nigeria.

08-25
52:35

#RanarHausa 2020 - Shirin Daga Taskar Hausa Daga Guarantee Radio 94.7 Kano

Shirin Daga Taskar Hausa inda aka tattauna da Farfesa Aliyu Muhd Bunza da Dakta Abdulƙadir L Koguna da kuma Dakta Muhammad Suleiman A., a kan Ranar Hausa ta Duniya wato 26 ga watan Ogusta 2020. Ku kasance da shirin a yau, Lahadi, ƙarfe 8 zuwa 9 na dare. Daga Guarantee Radio 94.7 Kano a ranar Lahadi Aug 23, 2020. Za ku iya saurara kai tsaye daga ko'ina a www.guaranteeradio.com

08-24
39:25

Kaucewa #LabaranBogi (Stopping the spread of #FakeNews in Hausa media)

Kai tsaye acikin shirin #ZararBubu da  @CDDWestAfrica ke daukar nauyin kawowa masu sauraro dan wayar da kai game da #LabaranBogi, Dr. Nura Ibrahim ke jawabi game da yadda za'a kaucewa labaran bogi a shafukan sada zumunta na zamani.   Related links:  https://twitter.com/CDDWestAfrica_H/status/1286959730716545026  https://youtu.be/aOgO9amMnl4   #ADainaYadaLabaranKarya #ADenaYadaLabaranKarya #StopFakeNews #StopSpreadingFakeNews #FakeNews #HausaFakeNews #FakeHausaNews #LabaranBogi

07-25
22:20

Asalin Ranar Hausa 2015 - Shirin VOA Hausa na Yau Da Gobe

Jamila Kabiru Fagge da Bashir Ahmad sun tattauna akan #RanarHausa August 26, 2015 Originally released August 28, 2015 on https://www.voahausa.com/a/2918757.html and https://soundcloud.com/voahausa/yau-da-gobe-134.

07-25
19:06

DW Hausa - Taba ka Lashe - Tasirin Wasan Kwaikwayo 2020.05.28

DW Hausa - Taba ka Lashe - Tasirin Wasan Kwaikwayo 2020.05.28 Mai gabatarwa: Fauziyya Dauda

05-28
09:40

Hausa News Headlines - Kanun Labaran Hausa na 2020.05.08

Full transcript: http://hausadictionary.com/hausaradio/20200508 1 Kanun Labaran DW Hausa - Shirin Yamma 08.05.2020 2 Kanun Labaran VOA Hausa - Shirin Dare 2030 UTC (30:00) - Mayu 08, 2020 3 Kanun Labaran RFI Hausa 20h00 - 20h17 GMT - Labarai 08/05 20h00 GMT 4 Kanun Labaran Talabijin na BBC Hausa 08/05/2020 5 Kanun Labaran Radio VOH 3 - 20200508

05-09
05:02

BBC Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.22

Show notes and transcript <> Cikakken bayanin wannan podcast din: http://bit.ly/BBCHausaSafe20190522

05-22
01:40

RFI Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin 07h00 Asabar 2019.05.18

Host (mai gabatarwa): Abdullahi Isa K'asashe masu k'arfin tattalin arziki da aka sani da G7 sun gudanar da taro a birnin Paris, taro da ya mayar da hankali zuwa ga batutuwan da suka shafi kiwon lafiya. Yayin da gwamnatin k'asar Venezuela da kuma 'yan adawa da ke cigaba da kai ruwa rana suka soma tattaunawa a Norway. Za ku ji cewa shafin sada zumunta na Facebook ya san da rusar wasu shafuka 216 na k'arya wadanda ake amfani da su domin rubuta kalamai ko kuma batutuwa da ba su dace ba zuwa wasu k'asashe. DRC: Gabbacin jamhuriyar demokradiyar Kongo a jiya Juma'a, har an fuskanci bori da ya kai ga rasa ran wani d'alibi mai shekaru sha biyu. Idan da sauran lokaci, da labaran wasanni (sports news). Read more at http://bit.ly/RFIHausa07h00Sat20190518

05-18
01:16

VOA Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17

Hosts (masu gabatarwa): Grace Alheri Abdu, Baba Yakubu Maƙeri US: Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya sanar da wani sabon tsarin dokan bakin haure, wanda zai [unintelligible] gurbin baki d’ayan dokan bakin haure a nan Amurka. US: A wata sabuwa kuma Donald Trump ya ce yana k'ir da zaton Amurka ba za ta shiga da yak'i a Iran ba a lokacin da ake k'ara samun tankiya a gabas ta tsakiya. Burkina Faso: Bayan haka, ministan harkokin wajen Burkina Faso ya yi kira ga k'asashen duniya su kafa wata had'akar yak'i da ayyukan ta'addaci kamar irin wadanda aka kafa su a k'asashen Iran da Afghanistan domin yak'i a yankin Sahel... Read more at http://bit.ly/VOAHausaSafe20190517

05-18
01:50

BBC Hausa News Headlines <> Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17

Host Mai gabatarwa: Aisha Sharif Baffa Yau ce dai ranar yak'i da cutar hawan jini, wato hypertension, ta duniya. Toh ko ya mutum zai kare kansa daga kamuwa da wannan cuta? "Farko, mutum ya zama cewa yana yawan motsa jiki. Sannan kuma a … Read More at http://bit.ly/BBCHausaSafe20190517 Thank you for subscribing. Share this episode.

05-17
01:34

DW Hausa Shirin Safe na 2019-03-01

DW Hausa Shirin Safe 01.03.2019 [1] Masana tattalin arziki da hada-hadar kudi a Najeriya, sun bada shawarar cewa ya kamata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta bada himma wajen raya tattalin arzikin kasar musamman a yankin arewacinta domin magance matsalolin da ke addabar yankin. Hosts: Muntaqa Ahiwa Nigeria: Cikin shirin za'a ji yadda masana suka soma baiwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shawara kan buƙatar zaburar da harkokin tattalin arziƙi, musamman ma na arewacin ƙasar da ke fama da matsaloli. Cameroon: Yara ne da ke fama da cutar nan ta HIV mai karya garkuwar jiki da ke cikin mummunar yanayi na rashin maganin rage raɗaɗin wannan cuta. Senegal: Zaɓen da aka kammala. North Korea: Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin sake zama da Amurka bayan tashi taron birnin Hanoi da aka yi ba tare da wata nasara ba. Amurka ta taya Najeriya murnar kammala zaɓe cikin kwanciyar hankali. Somalia: Wani harin ƙunar baƙin wake, ya salwantar da rayuka a ƙasar Somaliya.

03-01
01:20

ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019)

ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Abdullahi Salihu* Nigeria Elections 2019: Wasu daga cikin jami'an gwamnatin APC a Najeriya sun nuna ɓacin ransu matuƙa dangane da yadda ƙungiyoyi na dattijan arewa da ma wasu daga ɓangaren kudancin ƙasar suka nuna goyan bayansu ga ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyar adawa ta PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar. Ethiopia: Za mu duba yadda masana suke kallon kawo ƙarshen taron shugabannin ƙasashen Afrika, wanda aka gudanar a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha, da kuma abubuwan da taron ya cimmawa game da yiyuwar aiwatar da su a aikace. France: Za mu duba batun matakan da sojojin gwamnatin ƙasar France suka ɗauka na kare wanda ya juya mulki da suka ce an yi yunƙurin aiwatarwa a ƙasar Cadi. Iran, Lebanon: Za a ji sharhin [ unintelligible: bayan labaran? ] wadanda suka yi magana akan ziyarar wadansu harkokin wajen Iran a ƙasar Lebanon. Shirin Ko Kun San, Kaza a kan dame, shirin labaran wasannin mako. Venezuela: Shugaban ƙasar Venezuela ya ce ƙasar za ta zamai wa Amurka Vietnam matuƙar ta kai mata hari. Bahrain: An cika shekaru takwas da fara yunƙurin al'umma a ƙasar Bahrain. China: ƙungiyar kare hakkin bil Adama (human rights) na ƙasashen duniya sun zargi ƙasar China da take hakkokin musulmi.

02-14
03:04

BBC Hausa Shirin Rana (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Rana (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Sulaiman Ibrahim Katsina Nigeria Elections 2019: A yau ne a Najeriya aka shirya soma rarraba kayan aiki don zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe ranar Asabar. Suma masu sa ido, sun buɗe sansaninsu a yau. Wani kuma, wanda da alama ya fi kowa niyar zaɓen, tun jiya ya isa rumfar zaɓen. Inda yake shirin yin kwanaki uku yana jira kafin a soma kaɗa ƙuri'a."Tun jiya, ƙarfe goma sha ɗaya da rabi (11:30) na bar gida na. Na tattara kayana, na zo na zauna. Zan yi alƙawari kwana uku. EU: Tarayar Turai ta kammala wani tsari na wata doka, wadda ta shafi haƙƙin mallaka a intanet. Sai dai, akwai masu ƙorafi akan haka. Za mu ji ko su wanene. Labarin wasanni (sports).

02-14
01:07

BBC Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi Liberia: In gano gawar mutane biyar amma a mahaƙar ma'adinai ta gwal wadda ta rifta a arewacin Liberia a makon da ya wuce. USA, Yemen: 'Yan majalisar Amurka sun gabatar da uzurin da zai janyowa dakarun ƙasar su janye daga Yemen. Nigeria Elections 2019: Yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da zaɓe a Najeriya, masu larura ta musamman na ƙorafi kan jami'an tsaro a rumfunan zaɓe."Dubu biyu da sha biyar (2015), na je zan jefa ƙuri'a na, aka ce min ni in bi layi domin ban fi kowa ba. A bisa ga kundin tsarin dokoki na hukumar zaɓe. Mu akwai kulawa ta musamman. Idan muka zo, ba za mu bi layi ba. Sports: Real Madrid ta doke Ajax (Ayax) da ci biyu da ɗaya (2-1). Wasan farko, zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarin Turai. Sai kuma ana fara yabawa mai horasda Madrid ɗin.

02-14
01:19

BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi Nigeria: A Najeriya, an kai wa waɗansu tagwayen hare-hare kan ayarin gwamnan jihar Borno a lokacin yaƙin neman zaɓe a garin Gamboru. Nigeria Elections 2019: Jam'iyar PDP ta zargi gwamnatin APC da yi mata kwitingila na hana ta yin filin yin taro a Abuja: "Gashi bayan mun yi gangamin mutane, daga ko'ina sun taho, har da masu hawan jakuna da dawakai. Da muka je, muka tarar an sa kwaɗo, an hana." Sai dai kuma, ana ta ɓangaren, APC ta musanta wannan zargin: "Na farko dai, fili na gwamnati ne kuma na tabbata akwai ƙa'idoji wadda ake bi. Maganar cewa wai yau an hana su taro domin wani abu... tsoron faɗuwa ne, shi ya sa suke neman duk ta hanyar da za'a bi a tayar da hankali." Sudan: BBC ta bankaɗo wani wuri da ake tsare masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati tare da azabtar da su a ƙasar Sudan. Taƙaitaccen labarin wasanni.

02-14
01:26

VOA Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba. Nigeria: Ministan tsaron Najeriya, Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya ƙaryata jita-jita da ake yi na cewa jami'an ƙasar basu da kayan aiki."Ko ƙasar America, ko ƙasar Ingila (England), ko ƙasar Russia, ba za su ce suna da isasshun kaya da suka ishe su ba. Muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, wato EFCC, Ibrahim Mago, ya ce za su gurfanar da masu siyan da ƙuri'a da masu tada fitina lokacin zaɓr a gaban kotu. Ba shirin Nakasa. Ghana newspaper headlines <> sharhin jaridun Ghana. Saƙonnin masu sauraro na kan na'ura.

02-14
01:12

VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba. USA, Iran: Amurka tana tuhumar wata tsohuwar jami'ar sojan samanta wadda ta canja sheƙa zuwa ɓangaren Iran da yin mata leƙan asiri. USA: Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu bai tsaida shawarar rattaba hannu ko a'a kan ƙudurin bai ɗaya da jam'iyyu suka cimma ba wanda ya tanadi kuɗin gina katanga. USA: Majalisar wakilan Amurka mai rinjayin 'yan Democrats, ta kaɗa kuri'ar rage tallafin soji da Amurka ke baiwa gamayyar sojojin da Saudiya ke jagoranta a yaƙin Yemen. Nigeria Elections 2019: Manyan 'yan takarar shugabancin Najeriya, sun sake jaddada yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla. Nigeria: Gwamnar jihar Borno, Kashim Shettima, ya tsallake rijiya da baya a ƙauyen Lugumanu*."Mu mun ɗauka sojoji ne, ashe ba sojoji ba ne. Suna da kayan sarki kuma dukansu sun more..." Ba shirin Domin Iyali.

02-14
01:36

World Radio Day in Hausa (Ranar Rediyo ta Duniya 2019)

RFI Hausa's coverage of World Radio Day (0:00-1:16) DW Hausa's coverage (1:16-4:54) BBC Hausa's coverage (4:54-8:49)

02-13
08:49

Recommend Channels